Akalla mutane 12 ne ake fargabar an kashe a wata arangama tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a unguwar Zak da ke karamar hukumar Wase ta Jihar Filato.
Wani shugaban matasa a Wase mai suna Shapi’i wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin.
- Mahara Sun Sace Basarake Da Matar Aure A Kano
- Harbin Da Aka Yi Wa Ba-amurke Dan Asalin Afirka Ya Kunyata Amurka A Jajibirin Ranar Samun ‘Yancin Kanta
Ya bayyana cewa rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 da suka hada da ‘yan bindiga tara da kuma ‘yan banga uku.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Zak na da tazarar kilomita 40 daga garin Wase, hedikwatar karamar hukumar Wase.
A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ (OPSH) mai kula da harkokin tsaro a Filato da wasu sassan Kudancin Kaduna, Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin amma bai iya tantance adadin wadanda suka mutu ba.
Ya jaddada cewa Kwamandan da dakarun da suka dakile harin, sun zarce zuwa yankin Gajin Bashar domin yakar ‘yan bindigar da suka addabi yankin domin far wa jama’a, inda ya ce mutanen OPSH sun koma Gajin Bashar ne bayan sun samu kiran gaggawa.
Shugaban matasan ya bayyana cewa, “’Yan bindigan sun zo ne a kan babura a yawansu da safe, muna zargin sun kwana a wani daji da ke kusa da Zak.
“Lokacin da mutane suka fahimci cewa ‘yan bindigar sun isa garin, sai suka sanar da rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke Zak cikin gaggawa, inda suka yi gaggawar tattara dakarunsu zuwa yankin don dakile harin tare da ‘yan banga,” in ji Shapi’i.