Hukumar kiyaye aukuwar hadura ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta tabbatar da cewa mutane goma sha takwas (18) ne suka kone kurmus har ma ba a iya tantance su a wani mummunar hatsarin mota da ya faru gaf da kauyen Nabardo da ke cikin karamar hukumar Toro a kan babbar hanyar Bauchi zuwa Jos.
Hatsarin wanda ya kunshi motoci biyu motar kabu-kabu Toyota Hiace Bus mai lamba: FKE 688 YC da wata katuwar Tirela inda suka yi taho-mu-kara da juna.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kwamandan shiyya na hukumar, Malam Yusuf Abdullahi, ya ce, hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba, ya ce mutum 21 ne hatsarin ya shafa da suka hada da manyan mutane Maza 18 da kuma yara uku.
Ya nuna matukar takaicinsa bisa faruwar hatsarin duk da kokarin da suke yi ba dare ko rana wajen wayar da kan direbobi wajen ganin sun kauce wa tukin ganganci da gudun wuce kima amma sun kasa bin matakan da ake son su bi.
“Abun bakin ciki da takaici ne gaskiya. Kullum sai mun shafe sama da awa biyu muna wayar wa direbobi kai kan tukin wuce kima amma ina ba su ji.
“Yanzu ka duba wannan hatsarin da ya faru direban Bas din da dukkanin fasinjojinsa sun kone sun zama toka ba a ma iya gane kowa a cikinsu.
“Abun bakin cikin da ya faru da yammacin ranar Laraba mutum 18 suka mutu a mummunar hatsarin da ya faru kasa da kilomita uku zuwa kauyen Nabardo da ke kan hanyar Bauchi zuwa Jos.”
Ya ce, hatsarin ya faru ne sakamakon kauye wa ka’idojin tuki, “Mun fahimci cewa direban Bas din ya rasa shawo kan ikon motar ne wanda hakan ya sanya ya fita daga kan layinsa inda ya doshi inda Tirela take suka kara kuma kun san wurin ajiyar Mai na Hummer na kusa da injinta ne.
“Lamarin ya janyo karawa a tsakanin motocin biyu. Hatsarin kuma ya faru ne a cikin daji babu mutane a wajen balle su kai aikin gaggawa garesu. Dukkanin mutanen cikin motar ‘Bas’ da fasinjojinsa sun kone kurmus,” ya shaida.
Shugaban ya kara da cewa ‘yan sanda da jami’an ma’aikatar kula da walwala da jin dadi za su kula da yi musu jana’izar bai-daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp