Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina, ta ce an tabbatar da cutar kwalara ta kama mutum biyu a karamar hukumar Kusada, da ke jihar tare da wasu 118 da ake binciken lafiyarsu.
A cewar hukumar, tuni an ɗauki matakan fara amfani da tsarin kula da al’amuran da ke faruwa domin hana yaɗuwar cutar da sauran cututtukan da za a iya rigakafinsu a jihar.
- Rikicin Masarauta: Aminu Ado Ya Daga Tuta A Fadar Nassarawa
- Ina So A Gurfanar Da Ni A Kogi – Yahaya Bello
Daraktan kula da cututtuka na hukumar, Dakta Kabir Suleiman, a wani taron manema labarai a cibiyar bayar da agajin gaggawa na hukumar ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta É—auki matakan shawo kan cutar.
Dokta Suleiman ya jaddada cewa jihar ta shirya tsaf don daidaita bullar cutar, tare da samar da tsarin sa ido don gano masu kamuwa da cutar kwalara.
Hukumar yaki da cutar kwalara ta duniya ta bayyana Jihar Katsina a matsayin yankin da ke fama da cutar kwalara, inda ake ganin kananan hukumomi 10 suna cikin hatsarin kamuwa da cutar.
Hakan ne ya sa gwamnatin jihar ta tura kayayyaki zuwa dukkan ƙananan hukumomi 34 tare da samar da wuraren shayar da ruwa domin shawo kan lamarin.
Kazalika, hukumar ta bayyana cewa ta horas da ma’aikatan sa-kai 3000 don wayar da kan jama’a game da tsafta.