Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, ta ceto mutum 10 da aka sace daga hannun wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne.
A lokacin aikin ceton, mutane huɗu sun samu raunukan harbin bindiga kuma an garzaya da su asibiti don samun kulawa.
- Ya Kamata Wasu Kasashe Su Daina Goyon Bayan Masu Adawa Da Sin Dake Tayar Da Tarzoma A HK
- Sin Ta Yi Alkawarin Duba Batun Samar Da Mafita Ta “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu” Ga Taiwan
Amma, abin takaici, biyu daga cikinsu sun mutu yayin da ake ba su kulawa.
Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Laraba cewa ana ci gaba da neman waɗanda suka tsere yayin da bincike ke gudana.
Lamarin ya faru ne a ranar 24 ga watan Disamba, 2024, misalin ƙarfe 8:30 na dare, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa wata motar haya hari a Kwanar Makera, a kan titin Katsina zuws Magama Jibia, a ƙaramar hukumar Jibia.
‘Yan bindigar sun yi yunkurin sace fasinjoji 10 da ke cikin motar.
Bayan samun kiran gaggawa, DPO na Jibia ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa wajem, inda suka yi musayar wuta da su.
Sun samu nasarar daƙile yunkurin sace mutanen kuma sun ceto dukkanin fasinjojin.
Kwamishinan ‘yansandann Jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yaba da jarumta da jajircewar ‘yansandan, ya kuma umarci jami’an da su ci gaba da kokari.
Sannan, ya buƙaci jama’a su rika bayar da bayani kan duk wani abu da suka gani da ya shafi aikata laifi domin ɗaukar matakin gaggawa.