Wani gini mai hawa uku ya rufta a yankin Lekki da ke Jihar Legas, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu, yayin da aka ceto wasu mutane shida da munanan raunuka.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba.
- Sin Na Matukar Adawa Da Manufar Kariyar Ciniki Da Babakeren Amurka
- Kasafin Kuɗin 2025 Taswira Ce Ta ƙarfafa Tattalin Arziki Da Ci Gaban ƙasa – Ministan Yaɗa Labarai
Babban Sakataren hukumar, Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce har yanzu ba a gano musabbabin rushewar ginin ba, amma ana ci gaba da bincike.
“A halin yanzu, an tono gawarwakin maza biyu daga baraguzan ginin da ya rushe.
“An kuma ceto wasu mutane shida da suka samu munanan raunuka, inda aka kai su asibitin Marina General Hospital don ci gaba da jinya,” in ji sanarwar.
Hukumar LASEMA ta bayyana cewa tawagarta ta fara aikin ceto da bincike tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin agaji.
Haka kuma, an tura manyan motocin tono ƙasa don taimakawa wajen share baraguzan ginin da kuma ceto duk wanda ya maƙale a ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp