An kama wasu miyagu guda biyu da suka kware wajen yin fashi da makami na katin ATM a Kaduna.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Mohammed Jalige ya fitar, ya ce “A ranar 12 ga watan Yuni, 2023 da misalin karfe 1:40, wata mata ta bayyana cewa a ranar 10 ga watan Yuni, 2023 da misalin karfe 07:15 na safe, ta tafi bankin Jaiz, wanda ke kan titin Ali Akilu Kaduna domin amfani da ATM.
“A yayin da ta ke kokarin ciro kudi a injin ATM sai suka sauya mata katinta.
“Bayan ‘yan mintina kadan, ta samu sako an cire mata kudi a asusunta N404,000 daga bankin ta”.
DSP Jalige ya ce, a yayin bincike, jami’an hukumar leken asiri ta jihar Kaduna, sun kama Paul Agu Daniel, da Mike Ogah.
Ya ce, binciken da aka yi ya kuma gano cewa mutanen biyu sun damfari daya daga cikin wadanda abin ya shafa kudi Naira 948,000 ta hanyar amfani da katin ATM dinta.
Wadanda ake zargin na taimakawa ‘yansanda binciken da nufin cafke wasu masu aikata laifuka.
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yansandan ya yaba da kokarin jami’an tsaro na cafke wadanda ake zargin, tare da gargadin jama’a da su yi hattara da mutane a lokacin amfani da ATM.