Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa masu kada kuri’a miliyan 2,629,025 ne za su zabi sabon gwamnan Jihar Edo, a zaben da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.
Kwamishiniyar INEC mai sa ido da ke kula da jihohin Edo, Delta da Kuros Riba, Farfesa Rhoda Gumus, ta bayyana haka a ofishin hukumar da ke Benin a wajen gabatar da rajistar masu kada kuri’a ga shugabanni da wakilan jam’iyyun siyasa 16 da suka shiga zaben.
- Zaben Ondo: 20 Ga Mayu Ita Ce Ranar Mika Sunayen ‘Yan Takara Ta Karshe – INEC
- Laifukan Zabe Barazana Ne Ga Samun Sahihan Zabuka A Nijeriya – INEC
Gumus ta ce, “A bisa dokar zabe ta 2022, tilas ne INEC ta gabatar da rajistar masu zabe ga shugabannin jam’iyyun siyasa nan da kwanaki 30 kafin zaben. Muna kokarin bin doka da oda tare da aiwatar da ayyuka 10 cikin 13 da aka shirya gudanarwa a zaben gwamnan Edo.”
Yayin da take jaddada bukatar a gudanar da zaben cikin lumana, Gumus ta ce, “Bai kamata zabe ya zama ko a mutu ko a yi rai ba. Idan ba ku ci nasara ba a yau, kuna iya yin nasara a gobe. Matsaloli kullum suna tashi a ranar zabe. ‘Yan siyasa da magoya bayansu a Jihar Edo su guji tashin hankali.
“INEC ta shirya tsaf domin gudanar da zaben gwamna a Jihar Edo. Muna son masu ruwa da tsaki su bai wa hukumar zabe hadin kai domin ganin ayyukan kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe sun gudana yadda ake bukata. Ina ba da tabbacin cewa tare da goyon bayan jami’an tsaro za a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da walwala.”
Kwamishiniyar ta kasa mai sa ido kuma bukaci mazauna Edo da sauran ‘yan Nijeriya da su yi alfahari da kasarsu, kuma ka da su bari kabila ko harshe ya raba su.
Tun da farko kwamishinan zabe a Jihar Edo, Dakta Anugbum Onuoha, ya sake nanata cewa mutane 2,501,081 ne aka yi wa rajista a jihar domin zaben 2023, yayin da mutane 173,048 suka yi rajista a ci gaba da rajistar masu kada kuri’a daga ranar 27 ga watan Mayu zuwa 9 ga watan Yuni, 2024. Masu rajista 119,206, ciki har da wadanda suka sauya katin zabensu suka cancanta, wanda hakan ya kawo adadin masu kada kuri’a 2,501,081.
Onuoha ya ce za a dakatar da yakin neman zabe a ranar 19 ga watan Satumba, yayin da zaben gwamnan Edo zai gudana a ranar 21 ga watan Satumba.
Shugaban majalisar hadakan jam’iyyu a Edo, Greg Igbinomwanhia, wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar ‘Redemption’ na jihar, ya yaba wa INEC kan yadda ta ke kokarin gudanar da ayyukan zaben ba tare da tangarda ba.
Igbinomwanhia ya kara da cewa zaben gwamnan Jihar Edo da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba ba dole ne ya kasance an yi shi cikin ‘yanci da adalci da kuma zaman lafiya.
Ya bukaci shugabanni da magoya bayan jam’iyyun siyasa da su guji tashin hankali domin a zabi magajin Gwamna Godwin Obaseki ba tare da nuna adawa ba.