Mutane 3 ne aka rahoto sun rasu, yayin da wasu 15 suka jikkata a wani hadarin mota da ya afku a karamar hukumar Takai a jihar Kano.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, Saminu Yusuf Abdullahi a ranar Lahadi.
Ya ce hadarin ya hada da wata mota kirar Toyota Hilux mai dauke da mutane uku daga jihar Jigawa da wata motar bus dauke da mutane 15 daga Kano.
A cewarsa, nan take bayan da motocin suka yi karo, motar bus din ta kone kurmus bayan ceto wadanda abin ya rutsa da su, sai dai an rahoto cewa sauran fasinjoin sun samu raunuka daban-daban.
“Bayan samun labarin, mun aika da tawagarmu cikin gaggawa zuwa wurin da hadarin ya afku domin ceto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp