Aƙalla mutum uku ne suka rasu yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da wani bam ya fashe a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, a Jihar Borno, a ranar Asabar.
Bam ɗin da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka birne a kan hanya, ya tashi ne lokacin da wasu motocin fasinja ke wucewa.
- Hukuma Ta Haramta Bikin Ranar Kauyawa A Kano
- Me Ya Sa Manchester United Ta Fi Yin Kokari A Europa League?
Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “Wani mummunan abu ya fashe a hanyar Maiduguri zuwa Damboa a yau, inda aka tabbatar da mutuwar mutane uku, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka. Muna addu’a ga waɗanda suka rasu da kuma nema wa waɗanda suka jikkata waraka.”
Wannan ba shi ne karon farko da irin wannan hari ya faru a wannan hanya ba.
A makon da ya gabata, wasu ma’aikatan hukumar ilimi ta ƙaramar hukumar Damboa guda biyu sun mutu a irin wannan hari a hanyar Damboa zuwa Maiduguri.
’Yan ta’addan Boko Haram sun dawo da amfani da bama-bamai da suke birnewa a hanya domin kai hari kan matafiya da motocin da ke amfani da manyan hanyoyin Jihar Borno, abin da ya janyo asarar rayuka da dama a baya-bayan nan.
A halin yanzu kuma, dakarun sojin Nijeriya na ci gaba da kai farmaki a dazukan Sambisa da sauran maɓoyar ’yan ta’adda a faɗin jihar domin murƙushe su da kawar da su gaba ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp