Kimanin mutane hudu ne aka bayyana mutuwarsu yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban a wani turmutsitsi da ya afku sakamakon fashewar wani abu da ya haddasa gobara a kasuwar sinadarai da ke Onitsha, cibiyar kasuwancin jihar Anambra.
Lamarin da LEADERSHIP ta tattaro, ya afku ne da misalin karfe 12:45 na rana a ranar Talata wacce ta lalata kayayyaki da shaguna da aka kiyasta darajarsu da ta kai miliyoyin nairori a kasuwar.
An ce turmutsitsin ya faru ne biyo bayan fashewar wani abu da ya afku a wani bangare na kasuwar, wanda kuma yayi sanadin tashin gobara a kasuwar.
‘Yan kasuwan hudu da suka mutu da wadanda suka samu raunuka, suna kokarin tserewa ne amma sakamakon turmutsutsin da ya rutsa da su, suka rasa rayukansu, wadanda suka samu raunuka kuma an garzaya da su asibitoci mafi kusa.
Shugaban karamar hukumar Onitsha ta Kudu, Mista Emeka Orji, ya shaida wa manema labarai cewa, “kimanin mutane hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da mutane 12 suka samu raunuka, sakamakon fashewar wani abu a kasuwar sinadarai ta Onitsha a yau Talata, wanda ya haddasa gobara a yankin.