Kimanin mutane 5,140 da suka haɗa da Mata da Manoma da Limamai suka amfani da tallafin ɗan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Funtua a jihar Katsina., Sanata Bello Mandiya
Wannan bada tallafi na da nufin tallafawa al’umma domin samun hanyar dogaro da tare kuma kama sana’o’i gadan-gadan domin rage zaman kashe wanda a wannan yanki.
Haka kuma waɗanda mutane sun fito ne daga ƙananan hukumomi goma sha ɗaya da ke yankin na Funtua inda Sanata Bello Mandiya ke wakilta a majalisar dattawa ta Najeriya.
Kamar yadda ya bayyana wadanda za su amfana da wannan tallafi da aka kashe fiye da naira biliyan ɗaya sun fito ne daga ƙananan hukumomi goma sha ɗaya na shiyyar Funtua.
Daga cikin kayayyakin da aka raba sun haɗa da Keken Napped guda 138 da mashina korar Boxer guda 200 da injinan ban ruwa guda 750
Sauran kayayyakin sune takin zamani buhu 3,500 da na’urar sanyi (freezer) 202 da injinan markaɗe guda 350 sai motoci guda ɗaya ya ɗaukar marasa lafiya da kuma ta ‘yan makaranta.
Bello Mandiya wanda ya ce duk da bai samu tikitin takarar Sanata ba, amma dai baya da jam’iyyar da ta APC saboda haka ya yi kira ga magoya bayansa da su zaɓi APC tunda daga sama har ƙasa.
Haka kuma Sanata Bello Mandiya ya yi godiya da irin kauna da soyayya da jama’ar yankin Funtua suka nuna masa sannan ya yi fatan Allah ya kawo wanda zai yi abinda ya fi wanda ya yi.
Tunda farko da yake jawabi gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi yaba da ƙoƙarin ɗan majalisar wanda ya ce duk da rasa takara da ya yi hakan bai hana shi kawo Abin arziki ha jama’ar da da suka yi masa rana ba.
“Haƙiƙa jami’yyar APC na bukatar irin wannan taimako a irin wannan yanayi da ake tunkarar zaɓe wanda haka zai taimakawa jami’yyar APC wajan lashe zaɓe mai zuwa.
Gwamna Masari ya yi wa Sanata Bello Mandiya fatan alheri tare da kyakkyawan fatan cewa Allah zai duba zuciyarsa ya yi masa sakayya irin ta mutanen da suka taimaki al’umma.
Shima a nasa jawabin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa ya yaba da ƙoƙarin Sanata Bello Mandiya wajan kawo wannan abin alheri a yanki Funtua.
Bala Abu Musawa ya yi kira ga waɗanda za su amfana da wannan tallafi da su amfani da shi ta hanyar da ta da ce, sannan ya ce ya kamata su maida biki ta hanyar zaɓen jami’yyar APC daga sama har ƙasa a zaɓe mai zuwa