Sama da matasa maza da mata 800,000 a kananan hukumomin Funtua da Faskari suka amfana da tallafin kudi don yin sana’o’in dogaro dakai.
An ba da tallafin ne karwashin shirin tallafa wa rayuwar al’umma, domin rage fatara tsakanin mutane da ke yankin.
- NIS Fara Sintirin Fatattakar Baƙin Haure Mai Taken “Saukar Shaho” A Bayelsa
- Kotu Ta Umarci A Kamo Mata Dogarin Gwamna El-Rufa’i
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Lawal Sani Matazu, ya ce an tallafa wa mata 92 da kuma ba su horo a kan yin sabulu, kayan kamshi da man shafawa da sauransu kafin ba su tallafin.
Shugaban ya yi kirra ga matan karamar hukumar da su yi kokari wajen koyon yadda za su bi wasu hanyoyin zamani don dogaro dakai.
Ya ankarar da matan cewa, ya zama wajibi su koyi wasu hanyoyi wanda za su inganta sana’o’insu.
Ya ba da tabbacin cewa karamar hukumar za ta yi kokari don samar masu da masu sayen kayan da suka sarrafa. Shugaban ya ce an ba wasu matasan guda dari irin wannan tallafin.
A Faskari kuma, an ba matasa tallafin Naira dubu (1) kowannensu.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Bala Ado Faskari, ya ba da tabbacin cewa karamar hukumar za ta ci gaba da bayar da irin wannan tallafin a kowane wata.