Wani bincike da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gudanar, ya bayyana cewa fiye da mutum biliyan 1 ne a fadin duniya ke fama da tabin hankali ko suke fuskantar matsaloli da ke da alaka da kwakwalwa.
A ranar Juma’a ne WHO ta fitar da kididdigar, inda ta kuma kara da cewa abin da ya fi tayar da hankali a nan shi ne yadda ake samun akalla daya daga cikin matasa bakwai a duniya suna fana da tabin hankali.
- Yau Ake Gudanar Da Zaben Gwamna A Jihar Ekiti
- Peter Obi Na LP Ya Zaɓi Doyin Okupe Daga Ogun A Matsayin Mataimakinsa Na Wucin-gadi
“Al’amarin ya karu ne a shekarar farko da aka yi fama da annobar Korona, inda halin da aka shiga ya kara yawan masu fama da cutar da kashi 25 a cikin dari,’’ in ji rahoton.
WHO ta ce wannan shi ne kidididiga mafi yawa a tarihin hukumar a cikin wannan karnin, ta kuma shawarci kasashe da su dauki matakin magance lamarin.
Rahoton ya dora alhakin al’amarin a kan matsalolin tattalin arziki da yake-yake da sauyin yanayi da ake fuskanta a fadin dama na duniya.