Jami’an tsaron ta Cibil Defence da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, sun cafke wani mutum da ke shirin sayar da dansa mai shekaru takwas a kan kudi Naira miliyan 20.
Da yake gabatar da wadanda ake zargi a rundunar, Kwamandan Babban Birnin Tarayya, Olusola Odumosu, ya ce an kama mahaifin dan, Chinana Tali, tare da Pius Aondoakaa a ranar 10 ga Janairu, 2024 saboda hada-hadar sayar da Ushafa Tali.
- ‘Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Farmaki Ofishin ‘Yansanda A Katsina
- Gazawar Gwamnati Ta Tsananta Fatara Da Rashin Tsaro A Nijeriya –Atiku
Da yake bayyana yadda aka kama wadanda ake zargin, Odumosu ya ce, “Jami’an hukumar a FCT da hazikan jami’an leken asiri a cikin shirin da suka yi a watan Janairun 2024, sun kama wani uba da suka hada baki da wani yaro kan sayar da dan shekara takwas wanda ya ce dansa ne. akan kudi Naira miliyan 20 a FCT, inda suke ambaton yaro a matsayin “dan akuya”.
“Bayan bayanan da aka samu, nan take aka sanya wa wadanda ake zargin ido. Daya daga cikin wadanda ake zargin, Pius Aondoakaa, a kokarin neman karin kudi, bayan ya ki amincewa da Naira miliyan 12, inda ya nemi sama da Naira miliyan 20 .
“Ya kuma bayar da “Akuya” (wato yarinya) akan Naira miliyan15. Pius ya yi ikirarin cewa yana da da na sayarwa kuma mahaifin yaron yana so ya yi amfani da kudin da aka sayar don kula da sauran ’ya’yansa.”
Da yake bayar da karin bayani, kwamandan ya kara da cewa, “A bisa ga haka ne jami’an leken asiri na Babban Birnin Tarayya Abuja suka kama asalin mahaifin yaron Mista China Telpesa Solomon Tali zuwa Abuja a Janairun 2024. akan sharudan saye da biyan kudi Naira miliyan 20.
“Ma’aikatan sirri ne suka tarbe shi a wani lambu tare da dan nasa. An kamalla cinikin ne akan kudi Naira miliyan 20 daga nan ne jami’an tsaro suka shiga suka kama mahaifin mai suna Mista Chinana Tali mai shekaru 42 a karamar hukumar Logo ta jihar Benue inda suka kwato karamin yaron mai suna Ushafa dan shekara takwas. Tali.
“Wanda ake zargin, Pius Aondoakaa, namiji, dan shekara 29, daga Karamar Hukumar Logo ta Jihar Binuwe, wanda suka hada baki da mahaifin yaron, an kuma kama shi a ranar 12 ga watan Junairu, 2024. Dukan wadanda ake zargin ‘yan kabilar Tib ne kuma daga wani kauye mai suna R.C.M. Abeda Mbadyul a Karamar Hukumar Logo.”
Odumosu ya mika wadanda ake zargin ga hukumar yaki da fataucin mutane ta kasa domin ci gaba da bincike, tare da gurfanar da shi gaban kuliya yayin da za a sada yaron da mahaifiyarsa.
Da yake magana da manema labarai, mahaifin yaron ya yi ikirarin cewa matsalar rayuwa ce ta sa ya yanke shawarar sayar da dansa na hudu a kan Naira miliyan 20 don ba shi ikon daukar nauyin sauran ‘ya’yan nasa.
Ya ce, “Matsalar wahala ce ta sa na amince in sayar da dana a kan wannan kudi domin samun sukunin kula da sauran biyar din.”
Wakiliyar Hukumar ta NAPTIP, Oseafiana Chineyere, yayin da yake karbar wadanda ake zargin, ta ce, “NAPTIP za ta binciki wannan lamarin kuma sakamakon zai kasance mai kyau.”
A wani labarin kuma, Hukumar NSCDC Babban Birnin Tarayya ta kama wani matashi dan shekara 23 mai suna Yakubu Mati a watan Junairu, 2024 bisa laifin lalata igiya mai sulke a kan layin dogo na Idu.
An kama shi da faratanya, zarto, da kuma cocilan.