Shahararren mawakin siyasa a Nijeriya, Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya yi karin haske dangane da yadda yake gudanar da rayuwarsa; a wata hira da aka yi da shi a kafar yada labarai ta DW Hausa.
Mawakin, wanda ya shafe fiye da shekara 10 yana yin wakokin siyasa da na sarauta ya bayyana cewa; bayan harkar waka, yana kuma yin wasu sana’o’i da dama na yau da kullum.
- Shirin “Rawar Yingge: Wakar Jarumai”
- Kayan Abinci: Gwamnatin Nijeriya Ta Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Rage Farashi
Tun da farko dai, mawakin ya bayyana yadda yake samun wasu lokuta na rayuwarsa, yana wasannin motsa jiki; domin samun karin lafiya. Rarara ya sake jaddada maganr cewa, shi dalibin ilimi ne na addinin musulunci, wanda ya yi karatu a gaban mahaifinsa da ya riga mu gidan gaskiya.
Da yake amsa tambayoyi a kan ikirarin da wasu ke yi na cewa, sau da dama ya kan bijiro da wakoki a daidai lokacin da ake tsaka da shan wahala a Nijeriya, domin ya karkatar da hankalin mutane daga wahalar da ake ciki, sai ya buda baki ya ce; ko alama ba haka zancen yake ba, domin kuwa dukkanin wakokinsa yana yin su ne da dalili, idan ya yi waka; sai ta fado daidai gabar wani abu da yake faruwa a kasa, ba yana nufin yana yi ne; don kawar da hankulan mutane ba, in ji Rarara.
“Mutane da dama, na mayar da hankalinsu kan aibuna; maimakon abubuwan alhairan da nake yi, saboda haka; ko kadan ni ba na daukar wannan a matsayin komai face, hassada da wasu daga cikin mutane ke nuna min, amma idan kuma ka riga ka shiga gaban mutum, to fa babu wani abu da zai iya yi maka; wanda Allah Madaukakin Sarki, bai yi maka ba”, a cewar Rarara.
Dauda ya kara da cewa, babu wata waka da zai yi ba tare da an bukaci ya yi ta don isar da wani sako ba. Haka zalika, Shugaba Tinubu, ba shi da wani buri na tara dukiya a halin yanzu; illa kawai dai fatan barin tarihi mai kyau a matsayinsa na Shugaban kasa, kamar yadda sauran mazan jiya; irin su Sir Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa suka bari.
Dangane da abin da wasu ke dauka cewa, ana biyana makudan kudade; don yin wakokin da za su kawar da hankalin mutane, su sani cewa; na fi mayar da hankali a kan noma fiye da yadda nake yi wa harkar waka, dalili kuwa; ni manomi ne wanda a yanzu haka duk fadin yankin da nake, babu wani mai yin noma kamar ni.
Yanzu haka, ina noma a gona mai fadin Eka fiye da 100, sannan kuma; ina sa ran samun karin wata gonar mai girman Eka 500 da zan kara a kan wadda nake nomawa yanzu. Don haka, har Dam na sa aka yi min a cikin gonata, saboda noman rani; don haka kashi 70 na kudin shiga da nake samu yanzu, ya fito ne daga harkar noma, ba waka kamar yadda wasu ke tunani ba.
Daga karshe, mawakin ya ce; babu abin da yake jin dadi idan ya aikata, fiye da taimakon gajiyayyu, “Ina matukar jin dadi idan na taimaka wa wadanda ke bukatar taimako, domin abin da na yarda da shi shi ne, muddin ka taimaki wani; shi ma zai taimaki wani, daga karshe za a rasa wani wanda zai bukaci taimako a cikin mutane”, in ji Rarara.