A wannan makon mun kawo muku karashen tattaunawa da Ibrahim Gungu wanda aka fi sani da “Bawan Mata”. Inda a wannan karon ya bayyana wakokin da ya yi da kuma abin da ya shafi kalubale na sana’ar fim, kamar yadda suka tattauna da wakiliyarmu RABI’AT SIDI.
Mu koma ga batun waka, kafin ka bar waka ka yi wakokin sun kai kamar guda nawa, kuma a cikin wakokin ko akwai wadda ta zaga aka santa a gari?
Na yi wakoki da yawa, adadinsu zai kai 100, to amma wasu ma ba ni na rera su da muryata ba, akwai wadanda suka zagaya sosai kamar su, SO DA HAWAYE, wakar ta zagaya sosai kuma ta samu karbuwa. To amma ita Sunusi Anu shi ne ya rera ta, bayan an yi min kida a ‘studio’ na rera da muryata sai aka cire tawa shi ya dora tasa.
Tun bayan da ka bar harkar waka shin baka ji kana sha’awar komawa yi ba, ko kuwa yanzu ka fi son ka tsaya iya abin da ya shafi fim kawai?
Gaskiya ba na sha’awar komawa, na fi son in tsaya a bangaren fim kawai.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta game da fim?
To kalubale akan rayuwar dan’Adam ai ba a rasawa. Na fuskanci kalubale a kan wasu mutane wadanda har yanzu su basu fahimci meye fim ba, kuma ba su fahimci abin da fim ke nufi ba.
To ya batun nasarori fa, wadanne irin nasarori ka samu game da fim?
Alhamdulillah ma sha Allah, dukkakan wata nasara da mutum yake samu a dalilin fim Allah ya bani ita. Misali; nasara ta farko masoya, ka yi abu mutane su ce suna so kuma su rika bibiya suna yabawa kuma suna godewa, shima arziki ne, nasara ce, sannan na samu arziki da alkairi da kyaututtuka kala-kala a dalilin fim to kin ga sai dai in ce Alhamdulillah.
Ya ka dauki fim a wajenka?
Wani babban al’amari, saboda ni fim a wajena sana’a ce kuma hanya ce da nake isar da sakona ga al’umma iri daban-daban.
Wane buri kake son cimma game da fim?
To burina akan fim yana da yawa, kadan daga ciki, (1) in rika kai sakona na fadakarwa da ilimantarwa ga al’umma, (2) Allah ya kara min dauka ka a fadin duniya ya zama inda ma ba a sanni ba a sanni, (3) masu mugwayen hali in rika kakkawo karshensu domin ya zama izna ga mutane.
Wane ne babban abokinka a cikin masana’antar Kannywood?
Abokaina suna da yawa, amma dai wanda a ko da yaushe muna tare da shi shi ne Isah Bawa Doro.
Da wa ka fi so a hadaka a fim?
Gaskiya ne ba ni da zabi akan abokan aiki. Kowa aka hada ni da shi matukar shi ma ya fahimci aiki, to za mu yi tare kuma ‘Director’ zai samu abin da yake so.
Wa ya fi birgeka a cikin sauran jarumai?
Ni ai kowa nawa ne, duk wanda ya yi abin kirki akan aikin zai birge ni kuma zan jinjina masa.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai a rayuwa na farin ciki ko akasin haka, wanda ba za ka taba iya mantawa da shi ba?
Akwai na farin ciki sun fi adadin lissafi, wata rana ba na tunani ba na tsammani kawai sai wani masoyina ya kira ni a waya ya ce ga kyautar mota nan ya turo a kawo min, da fada min da yai da zuwan motar bai wuce awa biyu ba. Gaskiya na ji dadin wannan kyautar kuma ba zan taba mantawa da ita ba tun da a lokacin ma motar da ya bani, ba ni da ikon sayenta. Abin da ya taba faruwa da ni na rashin dadi a rayuwa ta wanda bana mantawa da shi shi ne rasuwar mahaifiyata, ta tashi lafiya kalau ba ciwo da Asuba ranar juma’a ta je bandaki ta dawo ta yi alwala a nan take Allah ya karbi ranta.
Mene ne burinka na gaba game da fim?
In sha Allah zan ci gaba da kokari ba ranar dainawa, sannan kuma in ci gaba da yin fadakarwa akan addini da kuma yadda rayuwa ya kama ta tafi.
To ya batun iyali shin akwai ko kuma tukunna dai?
Ina da mata da ‘ya’ya guda 3
To ya batun kari, shin za ka kara ko kuwa ba ka da ra’ayin hakan?
Wannan ai na Allah ne, idan na samu mai natsuwa mai hankali da ilimi da tarbiyya, kuma mai so na tsakani da Allah in sha Allah zan kara.
Misali wata a cikin abokan aikinka ta ce tana sonka za ta aureka shin za ka amince da hakan ko kuwa ba ka da ra’ayin aurar abokiyar aiki?
Kwarai kuwa, ina da ra’ayi idan Allah ya hada hankalinmu da ita ba wani matsala zan aureta.
Wacce shawara za ka bawa masu kokarin shiga harkar fim?
To Alhamdulillahi shawarar da zan basu ita ce duk mai sha’awar shiga fim to ya sani ita sana’a ce ta hukuri sai an yi hakuri ci gaba yake zuwa ba lokaci daya ba.
Ko akwai wani kira da za ka yi ga abokan sana’arka ta fim?
Ina kira ga abokan sana’a ta da mu kara jin tsoron Allah kuma ko mai mutum zai yi ya sani Allah zai tambaye shi. Mu ci gaba da aika wa al’umma sako na addini da nasiha da kuma fadakarwa a cikin ayyukan mu da muke yi na fina-finanmu.
Ko akwai wani kira da za ka yi ga gwamnati game da sana’arku ta fim?
Gwamnati ta kalli masana’artar Kannywood da idon albarka, ba kallon hadarin kaji ba. Su fahimci cewa mu fa taimakon su muke yi, saboda da yawa akwai wadanda suka gama makarantun Boko, ba su samu aikin yi ba a gwamnatance, amma sun samu aiki a masana’artar Kannywood, wanda hakan ya ragewa matasa zaman kashe wando a kasar nan. Amma da yawa za ki ji ana wasu abubuwa da suka shafi tallafa wa masana’antu a kasar nan, amma mu sai dai mu ji a salansa. Wani lokacin kuma sai dai mu ji takwarorinmu na Kudancin kasar nan (Nollywood) sun amfana mu an mai da mu saniyar ware. Don haka ina kara kira ga gwamnati da ta kara jawo ‘yan Kannywood a jikinta.
Me za ka ce da masoyanka?
To masoyana maza da mata ina godiya sosai Allah ya bar mu tare da ku Allah ya bar zumunci, kuma Allah ya kara daukaka mu ni da ku baki daya. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu baki daya Allah ya zaba mana shuwagabanni nagari.
Me za ka ce da ita kanta Jaridar Leadership Hausa?
Jaridar LEADERSHIP ja gayya ce a cikin kafofin yada labarai na Nijeriya. Bugu da kari LEADERSHIP wata kafa ce da ta kware wurin bincike na musamman tare da fitar da mutane duhu akan al’amurran da suke faruwa a kasar nan. Akwai mutane da dama wadanda suke zaune a cikin gida ko ‘office’ ba su zuwa ko ina, amma bibiyar LEADERSHIP ya sa duniya ta zamo a tafin hannunsu. Saboda kwarewarsu aiki mun gani, sun samu mabambantan karramawa, babu ruwansu, da akida ko bangarenci, gaskiya wannan gidan jaridar abun a yaba ne. Haka zalika ga dama da suke ba irin mu domin tofa albarkacin bakinsu, akan harkokinmu na yau da kullum.
Babu abin da za mu ce, sai dai Allah ya kara daukaka. Sannan Muna kira ga masoyanmu da su ci gaba da bibiyar LEADERSHIP Hausa musamman wannan shafi na Rumbun Nishadi, domin jin labaran da suka shafi fadakarwa, ilimantarwa, har ma da nishadantarwa, na gode.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Ina gaishe da daukacin ma’aikatan wannan gidan jaridar ta bangaren Hausa da Turanci, da kuma ke kanki, da ki ke kokarin gabatar da wannan shiri. Sannan godiya ga babban ‘Director’ Ibrahim Bala.
Muna godiya
To Alhamdulillah ni ma ina godiya Allah ya bamu nasara.