Shugaban Hukumar Tace Fina-finai Na Jihar Kano ISMA’IL MUHAMMAD NA’ABBA, wanda aka fi sani da AFAKALLA ya yi kira tare da karin haske ga masu shirya fina-finan Hausa.
Ya kuma bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen ganin an magance gurbatattun fina-finai da kuma gurbatattun mutanen da suke bata tarbiyyar al’umma. Wakilinmu YAKUBU FURODUSA ya zanta da shugaban ga kuma tattaunawar kamar haka:
Masu karatu za su so jin sunanka da dan takairaccen tarihinka
To ni dai sunana Isma’il Muhammad Na’abba, wanda aka fi sani da Afakalla.
Ni ne babban sakatare na hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano. An haife ni a garin Kano a 1970, na yi makaranta a Gwale kafin na dawo zuwa nan Daurawa Tarauni kenan, na yi karatuna a garin Kano.
Sannan kuma na yi gwagwarmaya sosai tare da kasuwa, domin da kasuwa na fara, na yi harkar mota, ita ce na fara kasuwanci akai na saye da sayarwa. Sannan na shiga harkar sana’ar fim a 2002, lokacin Kwankwaso kenan, sannan kuma na yi Furodusin din fina-finai da yawa irin su Muhsin, Fati ‘Yar Asalin mayubalwa, Karima, da dai sauransu. Kuma daga nan na rike mukamai da yawa na yi PRO na hadaddiyar Kungiyar masu shirya fina-finan ta Jihar Kano, na rike kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa, na rike shugabanci na shirya zabe da aka yi a 2007, sannan ina cikin wani hard work, na gwamnatin fim da Gwamnati Malam Ibrahim Shekarau ta samar, bayan wannan na zama ‘Code member’ a wannan hukuma ta tace fina-finai a 2011 zuwa 2015, sannan na zama babban Darakta a wannan hukuma a 2015 zuwa 2019, Sannan na kara dawowa a 2019 zuwa yanzu a matsayin babban sakatare, Alhamdulillahi ina da ‘ya’ya takwas Maza biyar Mata uku, sannan kuma ina da mace guda daya da nake tare da ita har yanzu.
A game da aikinku, kamar wadanne irin laifuka kuke kamawa?
Da farko dai akwai irin abubuwa na masu tallace-tallacen magani da suke shigowa gari, za ka ga suna saka lasifika, kawai shigowa ya yi Kano ba dan Kano bane, ba shida suruki ko suruka a garin nan ba shi da iyaye, ba shida ‘ya’ya, ba shida kowa a haka zai zo ya rika fadar kalaman batsa yana fadar maganganu wadanda za su zama cewa babu mutunci da tarbiyya a ciki, a haka zai ta fada zai ta maganganu ga mata ga yara mutum ya zo da iyalansa dole hukuma ba za ta bar wannan ba, kama irin wadannan mutane yana daya daga cikin ayyukanmu.
Sannan kuma akwai maganar gidajen biki da ake biki, akwai tsare-tsare da ake yi, tun da rayuwa dole akwai nishadi kuma bikin nan babu inda ba a yinsa, ana yi a gidan sarakai, ana yi a gidan malamai, ana yi a gidan masu mulki, don haka to wajibi ne kuma hukuma ta ce ga yadda tsarin za a yi.
Kano gari ne na Musulunci, gari ne na al’ada, gari ne da muke alfahari da shi, ta wajen tsaftace duk wani abu da zai bata tarbiyya, shi ya sa Allah ya taimaki Kano za ka ga harkar garkuwa da mutane ba ma ciki.
To wadannan na daga cikin hobbasa da irin wadannan hukumomi suke yi na wajen kare fushin Allah ga al’umma, ba abin da yake janyowa mutane matsala da tashin hankali da kuma shiga tasku irin na tsokano Allah, a yi abin da za a kalla a yi buris a kyale na sabo, ba mun ce sauran garuruwan ba sa iya nasu kokarin ba amma ba kamar Kano ba.
A Kano ake da Hizbah, a Kano ake da hukumar tace fina-finai kuma a Kano ake da Hukumar Shari’a, a Kano ake da zauren sulhu, duk wadannan zai nuna maka irin tsarin da Musulunci yake da shi da Tarbiyya. Sannan kuma a hakkin wannan garin namu ba a yarda ka je ma ka yi wasu abubuwan da ba su dace ba, za a kwabe ka, za a yabe ka za a nuna cewa wannan waye, sai an je har soron da aka haife ka ko aka haifi mahaifiyarka, ko aka daura auren mahaifinka da mahaifiyarka.
To wadannan abubuwan suna daya daga cikin dalilan da ya sa kano ta yi fuce ta fitar da hukumar tace fina-finai a 2001, kuma hukumar ta zama ta yi fice, ba don wani abu ba sai don kawai tsayawa da sauransu. Sau da dama za a kalle mu ‘yan kauye za a kale mu gidadawa duniya ta ci gaba, ya kamata a bar mutane su sake suna da ‘yuanci, ba haka bane, mu ‘yancin da Allah ya bamu shi ne ‘yancin da addininmu da al’adunmu suka bamu shi ne ‘yanci.
Don haka idan har ka zo kana yin wani abu wanda zai zama cewa ba za a iya ma daukar aure a baka ba to ka rasa ‘yancinka ka zamo wani irin zombi a cikin mutane, kai ba a nan ba, kai ba a can ba, su wadanda kake so ka yi koyi da su, ba su yarda kai nasu bane, ka baro taronka ka zama la’ila ha ‘ula’i.
To don haka ita hukuma tana saita dukkanin wasu abubuwa na wulakanta tarbiyyar mutanen wannan jiha domun inganta al’amuransu, na tarbiyya da addininsu, da al’adunsu, saboda Kano gari ne na Musulunci gari ne na al’ada shi ya sa za ka ga ba ma barin wadannan abubuwa, kuma duk shekara za ka ga Sarki ya yi hawa, ya fito da al’adu an fito ana hawan sallah karama, hawan Sallah babba, duk wadannan al’adu ne don al’umma masu kyau da zumunci na dauki yarana na kai su su sada zumunci, ka dauki naka ka kai su, wannan Kano ce take da wannan tsarin, don haka ba za mu bari ci gaban da ake ganin ya taho ba na duniya ko na wasu mawaka ko wasu ‘yan fim ko wasu wanene ko wasu abubuwan da za su zo su lalata wannan al’adar ba, don haka in ka ji ana rigima to wannan ce rigimar, in ka ji ana ah! dan me ya sa, to wannan ce ta sa.
Don haka duk me gaskiya duk me hali aka koma aka zaunar da shi aka ce za ka sa kanwarka na zai ba, za ka sa ‘yarka, ba zai ba, kai za ka yi za a zo ai sana’a kake, ko sana’a kake kar ka ci guba kar ka ba wa wani gubar.
To wadannan su ne rigingimu, kuma su ne matsalar kuma su ne abin da ake yi, mu kuma mun tsaya, Allah ne yake mana shi yake mana ba ma tsoron kowa, ba ma tsoron komai.
Yau shekarata kusan 12 a gidan nan tun lokacin Kwankwaso nake gidan nan, don haka na ga da yawa, na ji da yawa babu wani abu da zan gan shi yanzu ya tsorata ni a wadannan kwanakin da suka rage wanda muke ciki, saboda haka duk abin da muke yi Allah ya sani muna yin iya bakin kokarinmu ta wajen tsayawa mu ga abin da ya kamata, haka idan kuka tsaya za ku saka wadannan abubuwa cikin fina-finanku, ku yi kuma ku kalli al’ummar kuma ku kalli yadda za ku shigo da sakon domin kar sakonku ya zama koyarwa domin akwai matsalar da take faruwa wajen masu rubuta fim da kuma masu aikata fim din, ke yanzu kin rubuta fim ga labarinki, ga abin da kike so, shi kuma wanda ya zo darakta sai ya kalle shi ya juya ga yadda yake so labarin, don haka idan ka yi sauya wannan rubutun naki zuwa script, to akwai abubuwan da zai sako fijuwal, wanda zai fijuwalaizin din mutane wanda ba ya jin Hausa in ya kalla zai gane, misali kana kallon Indiya amma za ka gane wannan aure ake so a yi masa amma ita ba ta son mijin, a’a wannan iyayenta ne ta gudu ta bar su da dai sauransu.
Dole ne sai mun tsaya mun kalli wani bangare, kwanaki muna ta magana a kan wasu fina-finai da muka ce wadannan fina-finan bata tarbiyya suke yi ba dai-dai bane ba, saboda ka zo kana nuna cewa me laifi abin sha’awa ne ga al’umma, kuma duk duniya ba a fim haka, duk duniya ba a fim aikin me laifi ya zama abin sha’awa ga al’umma kyamarsa ake.
To amma yanzu ka zo ka yi fim ka ce ai gashi ya fito ana ma tafa shi da sauransu. Duk inda ka ga me laifi ko a fina-finai na turawa za ka gan shi cikin kunci sai ya sha wani abu sannan ya yi bacci, sai ya sha wani abu hankalinsa ya gurbata, amma nan me laifi ne zai fito ka za- kaza dan sanda ma tsoronsa yake, ba a haka wannan fim din ai da ka ji ana simgam in an cewa mutum singam za ki kenan kuma dan sanda ne saboda tsayawa kan gaskiya kuma kullum yana tsaywa har sai ya kai ga nasara.
To amma nan sai a nuna a’a ai kawai me lefi shi ne, a Scene daya biyu shi ne za a nuna wai yayu ‘yan laifi sanda sun kamashi, shikkenan sai ace daga karshe dai an kama shi. Idan aka duba wani fim 24 hours za a ga yadda aka yi fim din, wanda shi yake nuna cewa fim ba ana yjnsa bane dan ka tallata me laifi, a nuna cewa buwayayyene ya gagari kowa, no me laifi cikin kunci yake, me laifi cikin damuwa yake, me laifi cikin rashin jin dadin rayuwa yake, amma daga lokacin da ka dauka kana yi ne domin ka gyara ko mene dai sai ka ga su kuma mutane sun kasa gane tsarin daya kamata ka fito da shi ta wajen yadda za ka kallo cewa ga tsarin da za ka yi.
Wanne kira za ka yi ga masoyanka?
Ina yi musu fatan alkhairi, masoya har kullum babu abin da za ka yi illa fatan alkhairi, duk abubuwan da muke yi muna yi ne don a gudu tare a tsira tare, mu kalli tarbiyyar al’umma mu kalli tarbiyyar mutane, iyayenmu sun yi kokari wajen ganin cewa mun zama mutanen kirki, muna alfahari da su.
Masoya ku tsaya ku taimaka wa Gwamnati, mu tsaya mu taimaka wa wannan hukuma, kuma mu tsaya mu taimaka wa masu wadannan sana’o’i na shirya fina-finai da sauransu, inda suka yi daidai a cicciba su a basu kwarin gwiwa saboda gusar da wanda suke bara-gurbi a ciki, sannan mu kyamaci duk wani abu da za a yi ba daidai ba.