Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce yana da yakinin cewa zai kammala wa’adinsa na mulki ya bar Nijeriya fiye da yadda ya same ta a 2015.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa na bankwana da ya yi wa ‘yan Nijeriya a ranar Lahadi a Abuja yayin da yake barin ofis a ranar 29 ga watan Mayu.
- Zaki Da Dacin Mulkin Shugaba Buhari
- Mika Mulki: Yadda Buhari Ya Fara Damka Ragamar Shugabancin Nijeriya A Hannun Tinubu
Ya yi mika godiyarsa ga duk wadanda suka ba shi goyon baya da karfafa guiwa don taimaka masa wajen kawo wa kasar ci gaba.
Ya ce: “Ina kuma so in yi amfani da wannan dama domin na nuna godiyata ga dimbin ‘yan Nijeriya da suka bamu goyon baya da karfafa guiwa wajen taimaka mini wurin ciyar da Nijeriya gaba.
“Ba zan manta da miliyoyin ‘Yan Nijeriya da suka yi min addu’a a lokacin da nake rashin lafiya a wa’adin farko na mulki ba.
“A koyaushe ina yi muku addu’a da kuma Nijeriya ta ci gaba cikin aminci.
“Yayin da na nake kokarin barin ofis zuwa Daura, Jihar Katsina, na ji dadin cewa mun sake haifuwar Nijeriya ta hanyar daukar muhimman hanyoyin ciyar da kasar gaba, kuma ina da yakinin gwamnati mai zuwa za ta ci gaba da tafiyar da Nijeriya a kyakkyawar turbar da muka dora ta.
“Ina da yakinin cewa zan bar ofis 2023 fiye da yadda na samu Nijeriya a 2015.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp