Wata Malamar Jami’ar Oyo da ke jihar Akwa Ibom, Misis Christiana Pam, ta ce domin samun abincin da za ta rayu a irin wannan lokacin da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ke ci gaba da gudanar da yajin aiki, a yanzu haka ta rungumi sana’ar sayar da Dankalin Turawa domin samun abin kai wa baki.
A ranar 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin makonni hudu a matsayin gargadi bisa bukatun da suke, daga bisa ta kara tsawaita yajin aikin zuwa wasu watanni biyu a ranar 14 ga watan Maris. Sannan ta sake sanar da wasu karin makonni 12 a ranar 9 ga watan Mayu.
- Na Koma Sayar Da Dankalin Turawa Ne Sakamakon Yajin Aikin ASUU – Malamar Jami’ar Oyo
- Wasu Gwamnatocin Kasashe Sun Nanata Matsayinsu Na Tsaiwa Tsayin Daka Kan Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak A Duniya
Yajin aikin kamar yadda kungiyar ta ce, ta shiga ne sakamakon kasa ciki mata alkawuran da suka yi da Gwamnatin tarayya dangane da wasu tilin bukatun da take da su.
A hirarta da majiyarmu bayan da hotunan ta suka karade kafafen sadarwar zamani da ke nunata tana sana’ar, Pam ta ce, ta shiga halin matsatsi na rashin kudi sakamakon ita sabuwar ma’aikaciya ce wacce ba ta samu damar tara kudade masu yawan da za ta iya rayuwa muddin yajin aikin ya jima ba.
“Lokacin da aka ayyana yajin aikin wata guda, na yi tsammanin cewa ba za a wuce wannan lokacin ba za a dawo. Na dauka cewa kungiyar ASUU da gwamantin za su samu fahimtar juna kan bukatun ASUU, kwatsam sai kuma hakan ba ta faru ba, a takaice dai aka tsawaita yajin aiki.
A lokacin ne na fahimci tabbas ina bukatar daukan wani mataki. A farko-farkon yajin aikin na yi ta kashe kudade saboda ni sabuwa ce a lamarin don haka ban samu damar tara kudade masu yawan da zan iya rike kaina a lokacin yajin aikin ba. Bisa wannan dalilin sai na koma garinmu na asali jihar Filato domin neman mafita.
Na zo na shiga cikin matsalar kudi kai sai da aka zo gabar da ina cin bashi domin na samu yadda zan rike kaina da iyayena.
“Iyayena sun rungumi sana’ar noma hannu biyu-biyu tun ma kafin su yi ritaya a wajen aikinsu, don haka bayan da suka yi ritaya din ma sun cigaba da harkokinsu na noma. A lokacin da na koma gida, na bi su muka shiga harkar noma da tunanin cewa bayan wasu ‘yan makonni za a janye yajin aikin, sai ya zama tunanina na neman zama kamar abun wasa. Na shiga noman tare da iyayena muka share gona, aka yi shuka aka fara girbi har yanzu dai muna gida yajin aiki bai kare ba.
“Kan hakan na fara kokarin tunanin mene ne zan yi da zai ke kawo min kudin shiga ba kuma zan iya tambayar iyayena da suka yi ritaya kudi ba saboda su ma kansu suna fatan samu daga gareni. Daga bisani sai na yanke shawarar cewa na dukufa wajen Saida wasu daga cikin Dankalin da muka noma a gonarmu kuma na san za su yi daraja a Akwa Ibom.
“Da fari na fara saida Dankalin a Jos domin tara kudaden da zan yi jigilar Dankalin Uwa Akwa Ibom. Ta hakan na fara neman yadda zan rike kaina wannan dalilin ne ya sanya na shiga sana’ar saida Dankalin gadan-gadan.”
Da take bayani kan yadda jama’a suke fassara halin da ta shiga, ta ce ko a jikinta domin ita ta san halin da take ciki da kuma yadda za ta rufa wa kanta asiri kuma ta tsira da mutuncinta.