• English
  • Business News
Tuesday, June 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Na Sha Damarar Kawar Da Cakuduwa Da Maza A Bukukuwan Mata Zalla – Bahijja Kabara

by Abdullahi Muh'd Sheka
2 years ago
in Adon Gari
0
Na Sha Damarar Kawar Da Cakuduwa Da Maza A Bukukuwan Mata Zalla – Bahijja Kabara
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Bahijja Malam Kabara, Shugabar Gidauniyar Amirul Jaishi, ‘yar jarida mai gwagwarmayar sauya tunanin mata a wannan karni, ta bayyana wa shafin Adon Gari bababn fatan da take da shi na sauya al’adar cudanya tsakanin mata da maza a wuraren bukukuwa. Ko ta yaya za ta cimma haka? Ga tattaunawarta da wakilinmu na Kano, ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, kamar haka:

Za mu so ki gabatar wa da mai karatu kanki…

Sunana Bahijja Malam Nasiru Kabara, na yi karatun firamare a makarantarmu ta gida Ma’ahad Sheikh Muhammadu Nasiru Kabara, daga nan na koma firamare ta Dawakin Kudu, sai kuma makarantar ‘yan mata ta ‘Yan Gaya, daga nan na samu sukunin halartar makarantar koyon shari’a‘School for Legal Studies’a Kano. Daga nan ne kuma, sai na fara aiki da ma’aikatar yada labarai ta Jihar Kano. Bayan na fara aikin ne kuma na samu shiga budaddiyar jami’ar nan da aka fi sani ‘NOUN’, inda na yi karatun aikin jarida, aikin dana ke yi kenan har zuwa yanzu.

A bangaren karatun addini kuma kamar yadda aka sani, gidan maulana Sheikh Muhammadu Nasiru Kabara; gidan ilimi ne, a nan na samu sukunin yin karatun addinina a bangare daban-daban, wadanda suka hada da ilmin Kur’ani wanda har musabaka a mataki daban-daban na yi, na karanta bangaren hadisi da fikhu da sauran fannonin ilimi, alhamdulillihi.

Tun da gidan Kabara na da alaka da kokarin tallafa wa harkokin ci gaban al’umma, shin ko ke ma na da irin wannan fata?

Labarai Masu Nasaba

Wasu Kyawawan Ɗabi’u Da Suke Ƙarfafa Zamantakewar Aure

Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?

Wannan gaskiya ne, kuma dole na gode wa ‘ya’yan  maulana Sheikh Muhammad Nasiru Kabara mata, wadanda duk shawarar da na ba su cikin gaggawa suke karba tare da ba ni goyon baya, wannan tasa na kirkiri Gidauniyar Amirul Jaishi, wadda muke mayar da hankali wajen tallafa wa mata da masu bukata ta musamman, sai kuma masu karamin karfi musamman Muhammadawa Kadirawa, ayyukan wannan gidauniya sun hada da bayar da tallafin karatu, koyar da sana’o’in dogaro da kai tare da shiga cikin harkokin samar da maslaha tare da kyautata mu’amalar zamantakewa.

Mene ne ya ja hankalinki wajen fara hangen tsaftace harkokin bukukuwa, musamman idan aka dubi batun cudanya tsakanin maza da mata a lokacin  bukukuwa?

Alhamdu lillahi, duk wani mai kishin addini da kuma ganin yadda ake yi wa harkokin mutuntaka izgili, musamman yadda aka mayar da harkokin bukukuwa ta hanyar samun cudanya tsakanin mata da maza, wanda hakan wata babbar annoba ce, domin haduwar mata da maza annoba ce mai matukar ta da hankali da kuma yi wa harkokin addini karan tsaye, wanda ko shakka babu hakan ke jawo fushin Allah a daidai lokacin da ya kamata a yi masa godiya, yanzu an mayar da harkokin bukukuwa wurin cudanyar tsakanin maza da mata, wanda kuma Allah fushi yake yi da irin wadannan ayyuka.

Wane mataki kuke dauka don ganin kun kawo gyara a irin wannan hali da ake ciki?

Alhamdulillahi! Yanzu haka, na shiga shirin samarwa tare da horar da mata aikin DJ da daukar hoto da kuma MC, wadannan abubuwa su ne wadanda suka fi komai hadari a wuraren bukukuwa, za ka samu samari kadai ke yin kida a wuraran taron da mata ne zalla, mu kuma mata a duk inda muke da zarar mun ji kida shi kenan sai hankali ya koma can a rika rawa, wanda hakan ko kadan bai dace da tarbiyyar musulunci ba.

Wannan tasa zuwa yanzu na fara horar da mata aikin DJ, MC da kuma mai daukar hoto, wadanda idan taron mata ne su ne kadai za su gudanar da harkokin bikin tare da ‘yan’uwansu mata zalla, yanzu haka ni kaina na fara kokarin koyon aikin DJ, domin idan na iya shi kenan ni ma sai na shiga koyar da ‘yan uwana mata aikin na DJ, haka ita ma sana’ar daukar hoto da MC.

Wane kalubale kuke shirin fuskanta, musamman ganin ita wannan sana’a ta MC, DJ da daukar hoto, asalin masu ita za su kalli kamar kuna neman hanyar raba su da neman abincinsu?

Gakiya akwai babbar matsala, domin yanzu haka wanda duk na tunkara da nufin zai koya wa mata wannan sana’a ta DJ sai ya yi ta yi min yawo da hankali. Haka nan, su ma daga bangaren iyaye ina samun irin wannan kalubale, domin sai na gama magana da yarinya ta aminta da koyon aikin na DJ, kawai sai ka ji iyaye sun ce me zai sa mace ta kama sana’ar DJ, wallahi sai ka ga an sauya tunanin ‘yan matan. Amma alhamdulillahi, yanzu haka na samu gogaggaun makada Dj mata guda biyu, wadanda a halin yanzu sun iya komai, ni ma kuma yanzu zan fara koyon aikin na DJ, domin samun saukin koyawa sauran.

Mene ne fatan da kike da shi a kan wannan sabon tunani na tsaftace harkokin tarukan bukukuwa musamman a kasar Hausa?

Babban burina ko fatan da nake da shi shi ne, a wayi gari a ga duk wasu wuraren tarukan mata, ‘yan’uwansu mata ne ke yi musu kidan DJ, hoto da kuma MC. Sannan kuma, ina so maza su fahimci cewa; kowa da ka sani a wannan duniya iya rabonsa zai samu, yanzu haka akwai wasu gidajen manyan mutane a Kano da tuni sun karbi irin wannan shawara tawa kuma ni ce ke yi musu MC a wuraren bukukuwansu, hakan na kara farantawa Allah ganin an yi abin da Allah ke farin ciki ta fuskar kiyaye dokokinsa.

Wane abinci Malama Bahijja ta fi sha’awa?

Shayi ruwan bunu ko da madara, idan na sha shayi bukatata ta biya.

Wane irin sutura kika fi sh’awa?

Na fi sha’awar korayen tufafi.

Mene ne sakonki ga al’umma, musamman matan wannan zamani?

Sakona ba zai wuce na jawo hankalin mata a kan su ji tsoron Allah wajen dukkanin harkokinsu ba, haka su ma iyaye su yi kokarin yin kallon tsanaki ga tarbiyyar yaransu, domin amana ce Allah ya damka mana, sannan kuma wallahi ya yi alkawarin tambayar dukkanin abin da ya damka na manar tasa a gare mu. A karshe, ina fatan iyaye su ba mu hadin kai wajen barin yaransu, domin koyon wannan aiki da zai taimaka wajen tsaftace harkokin bukukuwanmu na yau da kullum.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: CakuduwaMataMaza
ShareTweetSendShare
Previous Post

FUDMA Za Ta Karrama Sarkin Bichi, Sarkin Daura Da Tsohon Gwamnan Katsina

Next Post

An Bude Rumfar Sin Kan Babban Taron Sauyin Yanayi Na MDD A Birnin Dubai

Related

Wasu Kyawawan Ɗabi’u Da Suke Ƙarfafa Zamantakewar Aure
Adon Gari

Wasu Kyawawan Ɗabi’u Da Suke Ƙarfafa Zamantakewar Aure

1 month ago
Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?

2 months ago
Mata Mu Tsaya Da Kafafunmu Kar Mu Tsaya Sai An Bamu – Khadeejah Abdullahi
Adon Gari

Mata Mu Tsaya Da Kafafunmu Kar Mu Tsaya Sai An Bamu – Khadeejah Abdullahi

4 months ago
Mata Mu Dage Da Neman Ilimi Da Neman Na Kanmu -Hassana Umar
Adon Gari

Mata Mu Dage Da Neman Ilimi Da Neman Na Kanmu -Hassana Umar

5 months ago
Mata Ku Dage Da Karatu Domin Tallafa Wa Rayuwarku Da Ta ‘Ya’yanku – Zahra’u Adam
Adon Gari

Mata Ku Dage Da Karatu Domin Tallafa Wa Rayuwarku Da Ta ‘Ya’yanku – Zahra’u Adam

6 months ago
Nijeriya Da Brazil Sun Cimma Yarjejeniyar Bunkasa Noman Zamani A Kasar Nan
Adon Gari

Halima Aliko Dangote Ta Nemi A Ba Mata Damar Shiga Harkokin Kasuwanci Yadda Ya Kamata

6 months ago
Next Post
An Bude Rumfar Sin Kan Babban Taron Sauyin Yanayi Na MDD A Birnin Dubai

An Bude Rumfar Sin Kan Babban Taron Sauyin Yanayi Na MDD A Birnin Dubai

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3

June 24, 2025
Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump

Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump

June 24, 2025
Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

June 23, 2025
EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2

EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2

June 23, 2025
Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana

Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana

June 23, 2025
Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Da Su Guji Tallata ’Yan Ta’adda Da ’Yan Bindiga

Gargaɗin Amurka: Gwamnati Ta Bayar Da Tabbaci Akwai Tsaro A Abuja

June 23, 2025
Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya

Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya

June 23, 2025
An Fara Kiraye-Kirayen Tinubu Ya Zaɓi Barau Jibrin A Mataimakinsa Na 2027

An Fara Kiraye-Kirayen Tinubu Ya Zaɓi Barau Jibrin A Mataimakinsa Na 2027

June 23, 2025
Za A Gudanar Da Taron Dandalin Davos Na Lokacin Zafi Karo Na 16 a Birnin Tianjin Na Sin

Za A Gudanar Da Taron Dandalin Davos Na Lokacin Zafi Karo Na 16 a Birnin Tianjin Na Sin

June 23, 2025
CMG Ya Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Kwamitin Shirya Gasar Wasannin Olympics Ta Milano Cortina Ta Shekarar 2026

CMG Ya Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Kwamitin Shirya Gasar Wasannin Olympics Ta Milano Cortina Ta Shekarar 2026

June 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.