Buba Galadima, wanda tsohon abokin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne, ya ce ya yafe masa duk abubuwan da ya yi masa.
Galadima na cikin waɗanda suka taimaka wajen kafa jam’iyyar APC kuma ya yi aiki tuƙuru domin ganin Buhari ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2015.
- Ministan Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Rasha
- Sin Na Maraba Da ’Yan Jaridar Duniya Da Su Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Harin Japan Da Na Tafarkin Murdiya
Amma daga baya, Galadima ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda gwamnatin Buhari ke tafiya, inda ya fara sukarsa a fili.
A wata hira da ya yi, Galadima ya kira APC jam’iyya mara amfani.
Galadima, ya ce shi ne mutum na huɗu da ya sanya hannu a takardar kafa APC, daga baya ya ce Buhari ya yaudari ‘yan Nijeriya.
Buhari ya rasu a ranar Lahadi a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, bayan fama da rashin lafiya.
Bayan jin labarin rasuwar Buhari, Galadima ya ce: “Na yafe wa Buhari duk abin da ya min a rayuwa.”
Za a binne Buhari a ranar Talata a garinsu na Daura da ke Jihar Katsina.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana birnin Landan tare da wata tawaga domin dawo da gawar marigayi Buhari zuwa gida Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp