Tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya ce, babban nasarorin da ya samu a lokacin da yake hugaban Nijeriya shi ne sanin Nijeriya da kulla mu’amala da abota da mutane daban-daban a matsayin salon shugabanci.
Ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da gidan rediyon FUT Minna Search FM, inda ya ce zai shawarci matasan Nijeriya ma su burin shugabancin Nijeriya da su nemi sanin mutane da fahimtar Nijeriya da kyau.
- IBB Na Kokarin Kawo Karshen Sabanin Da Ke Tsakanin Atiku Da Gwamnonin PDP ‘Yan 5
- Yanzu-Yanzu: Mataimakin Zababben Shugaban Kasa, Shettima Ya Gana Da IBB
Da aka tambaye shi dangane da irin nasarorin da ya samu a tsawon rayuwarsa, ya ce; “Na daya shi ne na yi wa kasa hidima sosai
Zan fada amma ba lallai ya gamsar da ku ba sai dai iya abin da zan iya fada shi ne; Na bar tarihi ya yi mana alkalanci.
“Na yi magana da mutanen kasar nan da dama. Ba ni da wata matsala da su, na kuma kara sanin kasar kasancewar ina tafiye-tafiye sosai. Na yi abokai a duk fadin Nijeriya kuma na yi tunanin hakan na daya daga cikin manyan nasarorin da aka samu,” cewar IBB.
IBB ya ce ya kamata matasan Nijeriya su yi iya kokarinsu wajen sanin Nijeriya da fahimtar kasar don su ne za su jagoranci kasar nan gaba.