Sanata Shehu Buba, wanda shi ne Shugaban Kwamitun Majalisar Dattijai kan tsaro da tattara bayanan sirri, ya ce ya ci karo da wani labari mai ban mamaki kan wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Augustan 2024.
Sanatan ya ce takardar mai ɗauke da sakon cewa Majalisar Masarautar Bauchi ta warware rawaninsa daga Sarautar Mujaddadin Bauchi a sakamakon zargin cin mutunci ko zagin Gwamnan jihar Bauchi a yayin wani gangamin yakin neman zabe a jihar.
- Masarautar Bauchi Ta Tuɓe Rawanin Sanata Kan Sukar Gwamna Bala
- Rikicin Warware Rawanin Tsohon Wazirin Bauchi Na Ci Gaba Da Daukar Sabon Salo
Sanata Buba ya bayyana martaninsa cikin wata takarda da ya fitar ranar Alhamis 15, ga Augustan 2024 da aka rabawa manema labarai ta kuma yaɗu a shafukan sada zumunta na yanar gizo, Inda ya bayyana cewa; “Ina amfani da wannan dama don bayyana wa jama’a cewa tun lokacin da na shiga harkokin siyasa ba na bin wani tsari na cin zarafin kowa idan ban da suka mai ma’ana ba tare da cin mutunci ko zagin kowa ba, wannan matakin shi ne tsarin da nake bi da nufin samar da ingantacciyar al’umma”.
“A lokacin da na saurari kalaman Gwamna lau Bauchi, Bala Muhammad da ya yi akan Shugaba Tinubu sai na ga hakan ya zama wajibi a kai na da na kare shugaban kasar daga yunkurin da ake yi na ɓata masa suna da zubar kimarsa da ƙoƙarin cusa kiyayyarsa a zukatan al’umma.” Cewar Buba.
Sanata Shehu Buba ya ce wannan shi ne iya abun da ya yi a lokacin yakin neman zaben da APC ta yi da ya halarta a kwanannan.
Sanatan ya ce sai kwatsam ya ji maganganun Gwamna Bala Muhammad akan shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, wanda kafafen yaɗa labaran ƙasar nan da dama suka rawaito, wan da ya ƙunshi fito da fito da zargi mara tushe da kuma kage, da amfani da kalamai da ka iya kawo barazana ta fuskar tsaro a ƙasa.
Sanatan ya kuma ƙara jaddada cewa zarge-zargen da Gwamna Bala Muhammad ya yi wa Shugaba Tinubu, kalamai ne na siyasa, ba su da tushe kuma ba su da wata cikakkiyar hujja da dalilai da za a dogara da su.
Sannan ya ce cikin kalamansa da ya yi ya musanta zargin da Gwamna Bala ya yi wa Gwamnatin Tinubu na rashin kula da aiki da Kare muradun al’ummar ƙasa. Tabbas ya ce ya zargi Gwamna Bala da aikata hakan.
Sanatan ya ce a jawabinsa da ya yi ya ce Gwamna Bala Muhammad ya karɓi Naira Biliyan144 daga asusun Gwamnatin Tarayya a Shekarar 2023 da kuma fiye da Naira Biliyan 47 daga watan Janairu zuwa yau, wanda ake sa ran a jumla ce za su kai Naira Biliyan 195 zuwa karshen wannan shekarar, na kima nemi bahasi akan cewa me Gwamnatin Bala Muhammad ta yi da wadannan makudan kudade.
Buba ya ce Shugaba Tinubu na yin iya bakin kokarinsa na ganin an samar da tsaro a faɗin Tarayyar Nijeriya da daidaita tattalin arziki da ganin an samu zaman lafiya tsakanin ‘yan ƙasa ba tare da samun rabuwar kai ba.
Buba ya ce shi kalamansa bai yi su da wata niyya ba face da kyayyakwar manufa da kare shugaban Tinubu.
A ƙarshe ya shawarci Majalisar Masarautar Bauchi da ta guji amfani da tunanin wasu, wanda hakan ka iya yi kawo cikasa wajen cimma manufofin masarautar.