• Leadership Hausa
Saturday, April 1, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Warware Rawanin Tsohon Wazirin Bauchi Na Ci Gaba Da Daukar Sabon Salo

by Khalid Idris Doya
3 months ago
in Rahotonni
0
Wazirin Bauchi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A makon jiya LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa masarautar Bauchi ta tsige Alhaji Muhammadu Bello Kirfi daga sarautar Wazirin Bauchi bisa zarginsa da rashin da’a da biyayya ga gwamnan Jihar Bala Muhammad.

Sai dai wakilinmu ya binciko cewa rashin fahimta ce ta siyasa ta gitta a tsakaninsu. Ko da yake shi Bello Kirfi da gwamnan jihar dukkaninsu ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne.
Rahotonni sun bayyana cewa, shi dai Bello Kirfi wanda dattijo ne kuma tsohon ministan ayyukan musamman a Nijeriya, kana dan gani kashenin Atiku Abubakar ne, ya kira wani taro inda ya bukaci jama’an Jihar Bauchi da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar amma a matakin gwamnan jihar kuma kowa ya zabi wanda yake so.

  • An Tsige Wazirin Masarautar Bauchi Kan Rashin Yi Wa Gwamna Biyayya

Ana ganin wannan dalilin ne ya fusata gwamna Bala Muhammad da har aka kai ga daukan matakin cire shi daga mukaminsa.
LEADERSHIP Hausa ta zanta da wani makusancin tsohon Wazirin Bauchi, Lawan Mukhtari Ladan, inda ya bayyana cewar babu komai a cikin lamarin illa batun da ya shafi harkokin siyasa da rashin fahimta irin ta siyasa.

“Wannan ba shi ne na farko da aka fara ba kuma dukkanin wadannan abubuwan da ka ga su na faruwa suna faruwa ne a kan gaskiya. Shi Alhaji Bello Kirfi mutum ne da yake da gaskiya yake da kaifi guda daya a dukkanin al’amuransa.

“Matsalar da ya samu a can baya aka dakatar da shi duka a kan irin wadannan abubuwan ne, zai zo ya fadi gaskiya ga gwamnati domin a samu gyare-gyare amma sai a zo ana samun matsaloli. Shi gwamna da ke jin giyar mulki sai ya yi abun da yake so.

Labarai Masu Nasaba

Bukatar Kare Hare-hare A Kan Likitoci A Sassan Nijeriya

Shinge 4 Da Sabon Gwamnan Zamfara Ya Tsallake Kafin Ya Doke Matawalle

“Yanzu dakatar da Baba Waziri da ya yi bai isa ya ce zai cire sunansa a zukatan jama’an Jihar Bauchi ba. Sannan kuma abun da ya faru shi ne, a matsayinsa na uban kasa ya ba da shawara cewa Bala Muhammad ya hakura da maganar takarar shugaban kasa tun da farko amma bai yi hakan ba tun daga lokacin ne fa aka fara samun matsala.

“Alhaji Muhammad Bello ya kira taro ya ce ga Allah ya kawo Atiku zai yi takarar shugaban kasa, yankinmu na Arewa Maso Gabas ba mu taba yin shugaban kasa ba amma yanzu ga dama ta samu don haka yana neman alfarman jama’a da su zabi Atiku.”

A nasa bangaren, kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya na Jihar Bauchi, Honorabul Abdulrazak Nuhu Zaki, ya ce sarakuna ne suka dauki matakin ladabtarwa.

“Sun kawo min takarda na ainihin sallamar Alhaji Muhammadu Bello Kirfi daga matsayin Wazirin Bauchi a wannan lokacin wanda tuni aka maye gurbi sa da Garkuwan Bauchi, Alhaji Mohammadu Uba Ahmed Kari da aka daukaka matsayinsa zuwa Wazirin Bauchi.
“Da an taba koranshi, Mai girma gwamnan Jihar Bauchi ya yi kokari ya maida shi ba tare da masarautar Bauchi tana so ba, ya je ya samu Mai Martaba Sarkin Bauchi ya ce ya yi hakuri da duk abun da ya musu a matsayin babansa, amma bai fasa abubuwan da yake yi ba.

“Wannan ne ya shi Mai girma gwamnan ya ce shi ma ya cire hannunsa kamar yadda suka niyyar cire shi, kuma daga yanzu ba ruwansa domin abun da yake musu ba daidai ba ne.”
“In ma ya zama yaya ne dai an cire shi, muna wa wanda ya samu kujerar fatan Allah ya taimakeshi ya rike sarautar da mutunci.

Domin kujera ce wacce take da bukatar mutum ya kame ya zama yana kiyayewa daga shiga harkar da ba irin ta su ba,” in ji Zaki.

Kakakin Jam’iyyar PDP, Alhaji Yayanuwa Zainari ya karyata duk wata zance da ke cewa akwai baraka tsakanin Atiku da Bala, inda yake cewa dukkaninsu suna karkashin lema daya kuma kowa na taimakon kowa a cikinsu.

Ya ce, “Ai ba abun da zai hada mai girma gwamnan jihar Bauchi da Atiku, Allah ya yi su a jam’iyya daya kuma kowa zai taimaki kowa, sannan duk inda muka je da gwamna neman alfarmar kuri’a sai mun fara nema wa Atiku a matsayinsa na dan takarar shugaban kasa, to ka ga ba wata matsala.

“Ita maganar sarauta in ka duba ma shi Waziri ba mai zaban sarki ba ne, babu hannun gwamna a kan takardar Waziri domin sarki ne yake nada Waziri. Don haka ka da a hada maganar sarauta da maganar siyasa.”
Sai dai kuma a gefe guda, Bello Kirfi ya maka gwamnatin Jihar Bauchi a kotu bisa abun da ya kira cire shi ba bisa ka’ida ba.

A wata sanarwar da mai magana da yawunsa, Barista Yakubu Bello Kirfi ya fitar ya bayyana cewa an yada wani labari na karya da aka ce Muhammad Bello Kirfi ya sha alwashin sai ya yi duk mai yiyuwa domin dakile zarcewar Bala Muhammad.
“Hankulanmu sun karkata kan wasu rahotonnin da aka wallafa a ranar 8 da 9 ga watan Janairun 2023 da aka nakalto cewa Alhaji Dakta Muhammad Bello Kirfi CON, na cewa zai yi duk mai yiyuwa domin cire gwamna Bala Muhammad daga kujerar gwamna ta hanyar hana masa nasarar zarcewa a zaben 2023 da ke tafe.

“Labarin sam babu gaskiya a ciki. A matsayinsa na musulmi, yayi imani da kaddara, kuma Allah ne mai iko, yana kuma ba da mulki ne ga wanda ya so ya karba daga hannun wanda ya so a lokacin da ya so.
“Cire shi da aka yi a matsayin Wazirin Bauchi kuma mambar majalisar sarkin Bauchi da aka yi a ranar 3 ga watan Janairu, gwamnatin Bauchi ce ke da hannu a ciki inda ta yi amfani da masarauta kuma hakan ya janyo ce-ce-ku-ce sosai a fadin jihar.”

Tunin dai Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu ya nada sabon Wazirin Bauchi, Alhaji Mohammadu Uba Ahmad Kari.
Nadin na Kari na zuwa ne bayan tunbuke rawanin tsohon Wazirin Alhaji Muhammadu Bello Kirfi bisa abun da aka ce rashin biyayya da mutunta gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Goron Juma’a

Next Post

Kotu Ta Fara Sauraren Shari’ar Raba Auren ‘Yar Ganduje A Kano

Related

Likitoci
Rahotonni

Bukatar Kare Hare-hare A Kan Likitoci A Sassan Nijeriya

21 hours ago
Shinge 4 Da Sabon Gwamnan Zamfara Ya Tsallake Kafin Ya Doke Matawalle
Rahotonni

Shinge 4 Da Sabon Gwamnan Zamfara Ya Tsallake Kafin Ya Doke Matawalle

6 days ago
Darussan Da ‘Yan Siyasa Za Su Koya A Zaben 2023
Rahotonni

Darussan Da ‘Yan Siyasa Za Su Koya A Zaben 2023

6 days ago
NLC Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Man Fetur Da Takardun Kudi 
Rahotonni

NLC Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Man Fetur Da Takardun Kudi 

3 weeks ago
Gudummawar Hajiya Hadiza Bala Usman Wajen Bunkasa Rayuwar Matan Nijeriya
Rahotonni

Gudummawar Hajiya Hadiza Bala Usman Wajen Bunkasa Rayuwar Matan Nijeriya

3 weeks ago
Sin Ta Taya Murnar Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Nijeriya
Rahotonni

An Fara Zawarcin Mukaman Siyasa A Gwamnatin Tinubu

3 weeks ago
Next Post
Kotu Ta Fara Sauraren Shari’ar Raba Auren ‘Yar Ganduje A Kano

Kotu Ta Fara Sauraren Shari'ar Raba Auren 'Yar Ganduje A Kano

LABARAI MASU NASABA

An Yanke Wa Wasu ‘Yan China 2 Hukuncin Daurin Shekaru 12 A Sakkwato

An Yanke Wa Wasu ‘Yan China 2 Hukuncin Daurin Shekaru 12 A Sakkwato

March 31, 2023
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Irin Su Na Farko A Duniya

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Irin Su Na Farko A Duniya

March 31, 2023
Zababben Gwamnan Katsina Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Matsalar Tsaro Zai Fi Bai Wa Muhimmanci 

Zababben Gwamnan Katsina Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Matsalar Tsaro Zai Fi Bai Wa Muhimmanci 

March 31, 2023
Kasar Sin Ta Bayar Da Shawarwari Dangane Da Yadda Za A Aiwatar Da Sanarwar Vienna Yadda Ya Kamata

Kasar Sin Ta Bayar Da Shawarwari Dangane Da Yadda Za A Aiwatar Da Sanarwar Vienna Yadda Ya Kamata

March 31, 2023
Mutum 14 Sun Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano Kan Aikata Fashi Da Makami

Mutum 14 Sun Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano Kan Aikata Fashi Da Makami

March 31, 2023
Ana Fatan A Hada Kai Wajen Shawo Kan Kalubalen Dake Addabar Duniya

Ana Fatan A Hada Kai Wajen Shawo Kan Kalubalen Dake Addabar Duniya

March 31, 2023
Ba Zan Tsoma Baki A Gwamnatin Abba Ba –Kwankwaso

Ba Zan Tsoma Baki A Gwamnatin Abba Ba –Kwankwaso

March 31, 2023
Taron Kolin Demokuradiyya Na Amurka Ya Shaidawa Duniya Ma’auni Biyu Da Amurka Ta Dauka Kan Batun Demokuradiyya

Taron Kolin Demokuradiyya Na Amurka Ya Shaidawa Duniya Ma’auni Biyu Da Amurka Ta Dauka Kan Batun Demokuradiyya

March 31, 2023
Har Yanzu Ni Ke Da Cikakken Iko A Matsayin Gwamnan Kano —Ganduje Ga Abba Gida-Gida

Har Yanzu Ni Ke Da Cikakken Iko A Matsayin Gwamnan Kano —Ganduje Ga Abba Gida-Gida

March 31, 2023
Boao: Kasar Sin Ta Karfafa Gwiwar Kasa Da Kasa

Boao: Kasar Sin Ta Karfafa Gwiwar Kasa Da Kasa

March 31, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.