Fagen siyasar Nijeriya ya fara dumama tun daga ranar Lahadin da ta gabata, yayin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sanar da tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa duk kuwa da cewa dukkansu biyun musulmi ne. Lamarin da ake ganin ya saba wa al’adar shugabancin Nijeriya a mafi yawan lokuta ta yadda ake hada Musulmi da Kirista.
Wannan hadin ya tayar da kura da dumama yanayin ciki da wajen jam’iyyar mai mulki ta APC.
Tinubu ya shelanta zabin Shettima a lokacin da ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura sa’ilin ziyarar barka da sallah a mahaifar Buharin ta Daura da ke Jihar Katsina.
LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewa, tun kafin sanar da zabin musulmi a matsayin mataimakin Tinubu, an yi ta samun masu korafi da nuna rashin gamsuwa da cewa musulmi da musulmi ne za su yi takara a babban jam’iyya da ke mulki a kasar nan, kodayake Tinubu ya murza idanunsa, ya zabi musulmi a bisa dogaro da cewa musulmai ke da rinjaye a arewacin kasar nan.
Kafin Tinubu ya sanar da Sanata Kashim Shettima, sai dai Ibrahim Masari ya sanar da janyewa da yin murabus daga nadinsa a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa da Tinubu ya yi da fari.
Masari ya ce, ya ajiye nadinsa ne bayan neman shawarwarin masu ruwa da tsaki ciki har da shi Tinubun daga baya ya sanar da mambobin jam’iyyar APC. Daga nan Masarin ya ce, zai mara baya dari bisa dari ga nasarar Tinubu a 2023.
Sanata Shettima wanda ya fito daga shiyyar arewa maso gabas (shiyya daya da dan tatakar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar) kafin sanar da shi a matsayin mataimakin Tinubu, shi ne daraktan yakin neman zaben Tinubun a zaben fitar da gwanin shugaban kasa na APC.
Korafe-korafe da yamutsi sun kunno kai a ciki da wajen jam’iyyar inda wasu ke ganin sam bai dace a hada musulmi da musulmi su yi takara ba, a gefe guda kuma wasu na ganin muddin in ba hakan Tinubu ya yi ba to zai rasa kuri’in ‘yan arewa da dama.
Kan hakan, kungiyoyin Kiristoci a shiyyar arewacin Nijeriya, sun ayyana cewa, tabbas ba za su yi kamfen wa Tinubu ba domin zabin da ya yi wa musulmi a matsayin mataimakinsa.
Kiristocin a wani jawabin bayan taron da suka fitar a ranar Talata bayan wani zaman gaggawa da suka kira a Abuja, sun nuna cewa shigo da addini da APC ta yi alami ne na za ta rasa kuri’in kiristoci da dama.
Jawabin bayan taron wanda Farfesa Doknan Sheni (Shugaba) da Janar Ishaka Bauka (Sakatare) da Farfesa Saudi Ibrahim, suka sanya wa hannu, ta nunar da cewa kungiyar ta ce zabin musulmi da musulmi da APC ta yi, ya nuna wariya ga kiristocin arewa mafi muni.
Daga nan sun bai wa APC daga nan zuwa ranar 15 ga watan Yuli da ta gaggauta sauya Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takara ko ta fuskaci tirijiya daga gare su.
Bayanin na cewa, “Kiristoci ‘yan siyasa daga jihohin arewa 19 da suke cikin APC sun zauna a Abuja inda suka cimma matsayar tir da matakin yin amfani da tikitin musulmi da musulmi.
“Ganawar tamu ta cimma matsayar cewa, mu kiristoci da muke cikin APC tabbas ba a mana adalci ba ko kadan, don haka ba za mu yi kamfen wa tikitin Musulmi da musulmi ba.”
Suka ce, Nijeriya kasace mai addinai mabanbanta kuma kamata ya yi ake la’akari da kowa cikin tafiyar da lamura ba wai kwasan komai a bai wa musulmai ba.
“Rashin yi wa kiristocin arewa da kasa adalci, za mu dauka APC ta zama jam’iyyar addinin Musulunci ne kawai, don ba a yi tikitin musulmi da musulmi a 2015 ba, to me ye sa hakan zai faru a 2023?.
“Kiristoci a arewa da ma kasa dole kawai su damu, bisa la’akari da cewa, shugaban jam’iyyar APC musulmi ne, mataimakinsa a shiyyar arewa musulmi ne, shugaban majalisar dattawa musulmi ne, mataimakin kakakin majalisar wakilai da shi kakakin majalisar dukkansu musulmai ne kuma a zo a ce dan takarar shugaban kasa musulmi mataimakinsa musulmi.”
“Muddin ba a canza mataimakin dan takarar shugaban kasa da kirista ba, to tabbas za a fuskanci tirjiya daga wajenmu.”
Daga nan kiristocin sun jawo hankalin APC ta kula da batun hadin kan kasa da ‘yan kasa a maimakon bijiro da abubuwan da za su kawo rashin fahimta a tsakani.
Kazalika, shugaban kungiyar kiristoci reshen jihar Borno, Bishop Mohammed Willians Naga ya musanta mara wa tikitin musulmi da musulmi baya, ya ce yarfe aka masa shi bai mara wa Shettima baya kan nadinsa a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa ba.
Naga na musanta wani labari ne da wasu kafafe suka yada suka jingina gare shi bayan da kiristoci daga yankin Maiduguri suka fara nuna shakkunsu kan labarin da suka ga an ce shugaban CAN din ne ya fada na mara wa zabin Shattima baya.
Bishop Naga, shugaban Cocin PBCC a jihar Borno, ya nuna damuwarsa bisa labarin, inda ya ce wasu ne suka ciro daga wata hira da ya taba yi da ‘yan jarida a ranar 3 ga watan Afrilun 2017 lokacin da Kashim Shettima yake matsayin gwamna.
Ya kalubalanci wadanda suka yada bayanin nasa da cewa su fito su shelanta idan har sabuwar magana ya yi da ‘yan jarida, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu suka kauce wa ka’idar aikin jarida domin kawo shakku a zukatan al’umma.
Sai dai duk da wannan sukar, APC ta fito ta kare zabin da ta yi wa musulmi da musulmi a masayin masu mata takara, inda ta ce ita fa ta zabi wadanda za su iya kawo mata nasara ne kawai da za su iya cin zabe.
Mataimakin shugaban APC a shiyyar Arewa maso yamma, Salihu Lukman a ranar Talata ya shaida hakan lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a Kano bayan wani taron da suka yi na jam’iyyar domin rarrashin mambobin jam’iyyar da suke da wani kulli a ransu a shiyyar arewa maso yamma.
Ya ce, babu wani abu na rashin daidai a amfani da tikitin musulmi da musulmi a gabar da ake nema wa kasar mafita daga halin da ake ciki, “Idan musulmi da musulmi ne za su iya kawo wa jam’iyyarmu nasara, abu mai matukar muhimmanci shi ne a duba yadda za a samu nasara a kuma aiwatar da ita, na biyu kuma a nemo wadanda za su iya kai jam’iyyar ga tudun-mun-tsira.”
A wani bangaren kuma, walikinmu ya labarto cewa akwai rade-radin da ake yi na, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya nuna rashin jin dadi da gamsuwarsa da zabin Musulmi da musulmi a matsayin ‘yan takarar APC, inda ya yi gargadin cewa irin wannan hadin ba zai yi tasiri ga al’ummar kasa ba.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce Osinbajo ya nuna adawarsa matuka da bijiro da tikitin musulmi da musulmi a cikin jam’iyyarsu ta APC.
Ya nuna cewa, zabin musulmi da musulmi tamkar kawar da kiristoci ne a gefe guda, don haka bai amince da zabin ba.
Yana daga dumamar da yanayin siyasar kasar ya yi kan wannan batu, yadda wasu kushohin jam’iyyar ta APC ke ci gaba da murabus daga matsayinsu na mambobin jam’iyyar. Zuwa lokacin rubuta wannan rahoto dai, wadanda suka yi murabus din sun hada da: Prince Tonye Princewill, tsohon shugaba a zamanin mulkin soja a Abia, ABM Frank Ajobere da wasu da ake tunanin za su bi sawu.
Masu ficewa daga jam’iyyar sun nuna cewa rashin adalcin da aka yi wa kiristocin kasar nan na daga cikin dalilansu na ajiye jam’iyyar a gefe.
A daidai lokacin da wasu ke ficewa daga jam’iyyar bisa nuna fushinsu da zabin musulmi da musulmi a matsayin ‘dan takaran shugaban kasa da mataimaki, shi kuma wani fitaccen dan kasuwa kuma dan siyasa, Adamu Garba dawowa ya yi cikin jam’iyyar bayan ya fadi daga takara a jam’iyyar YPP.
Ya nuna goyon bayansa dari-bisa-dari ga zabin Shettima a matsayin mataimakin Tinubu, ya kuma nuna cewa za su mara baya sosai wajen cimma wannan nasarar, “Ba maganar addini ake ba, waye da waye za su iya kawo wa jam’iyyar nasara, don haka zabin Shettima zabi ne da tabbas jama’a da dama za su zabi APC a arewa.” In ji shi.
Wasu Al’amura Da Suka Faru A Ziyarar Barka Da Sallah Ga Buhari.
Yana daga cikin abubuwan da suka faru a yayin ziyarar gaisuwar barka da sallah ga Shugaba Buhari, maganar da aka ce ya furta ta ya kagara wa’adin mulkinsa ya cika ya sauka ya huta.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna cewa zama a kujerar shugaban kasa ba abu ne mai sauki ba, don haka ya ce ya kagu wa’adin mulkinsa ya cika ya sauka ya huta.
“Na matsu na tafi. Zan iya fada muku abin da wuya. Ina godiya ga Allah da kuma jama’a a bisa yabawa da irin sadaukarwar da muka yi,” in ji shugaban kasa a mahaifarsa ta Daura d ake jihar Katsina.
Buhari ya ce ko a baya-bayan nan yana tausaya wa Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyema, wanda yake yawan tafiye-tafiye yana barin iyalansa duk domin yadda za a samar wa kasar nan ci gaba mai daurewa.
Buhari ya ce idan aka yi duba kan bayanan da ke kasa, gwamnatinsa ta yi kokari sosai idan aka kwatanta da ta baya, musamman a fannin gina al’umma da ababen more rayuwa, ya nuna cewa gwamnatinsa ta ciri tuta.
Duk da ya nuna mulkin da wuya, shugaban kasan ya yi fatan alkairi ga wanda zai gaje shi a mulkin kasar nan, “Badi war haka, zan kammala ragowar wa’adina, kuma zan yi bakin kokarina a ragowar watannin da suka rage min,” in ji shi.
Shugaba Buhari ya nemi masu rike da mukaman siyasa da su dinga taimakon ‘yan Nijeriyar da ke neman damarmaki. Ya ce, ta hanyar taimakon juna za a iya rage wasu matsalolin da suke damun kasar nan.
Daga nan, ya tabbatar wa gwamnonin cewa, shi idan ya kammala wa’adin mulkisa garinsa ta Daura zai koma da zama ba gidansa da ke Kaduna ba.
“Nan da wata 10 zuwa 11, nan (Daura) zan dawo, ina da babban gida a Kaduna, amma ya yi kusa da Abuja,” duk kuwa da cewa a gidansa na Kadunan ya saba rayuwa kafin ya zama shugaban kasa, amma Buharin ya ce bayan ya kammala mulkinsa ba nan zai koma ya ci gaba da zama ba.
Dangane da matsalolin tsaro da suke faruwa musamman a yankin arewa maso yamma, Buhari ya ce gwamnatinsa na kokari matuka kuma za ta ci gaba da kokarin kawo karshen abin. Ya nuna cewa ana samun gagarumar nasara kan matsalar ta tsaro a shiyyar arewa maso gabas da kudu maso kudancin kasar.
Daga bisani, ya nemi al’ummar yankin kudu maso kudu da su daina lalata dukiyoyin kasa, wanda hakan ke shafar zamantakewrsu da ci gaban kasa musamman ma yankunan nasu.
Da ya ke maida jawabi a yayin zaman, shuganan Kungiyar Gwamnonin APC, Abubakar Atiku Bagudu, ya gode wa shugaban kasar bisa irin salon mulkinsa da ya bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma irin nasarorin da APC ta cimma.
Gwamnonin jam’iyyar APC sun bayyana goyon bayansu ga Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar a zaɓen 2023, yayin ganawar tasu da Shugaba Buhari.
Shugaban gwamnonin na APC Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da gwamnan Imo Hope Uzodimma wadanda suka yi magana a madadin sauran gwamnonin sun ce da yawun bakinsu aka amince da Kashim a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.
Sun kuma yi alkawarin yin aiki domin tabbatar da jam’iyyarsu ta APC ta yi nasara a zaɓen 2023.
Baguda ya kara da cewa, “Za mu yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar APC a 2023. Muna da dalilai na yin aiki sosai domin nasarar jam’iyyarmu.
Sauran gwamnonin da ke cikin tawagar akwai Gwamnan Katsina Aminu Masari da Abdullahi Ganduje na Kano da Gwamnan Neja Abubakar Bello da na Nasarawa Abdullahi Sule. Akwai kuma Malam Nasir El-Rufai, Gwamnan Kaduna da Kayode Fayemi na Ekiti da Simon Lalong na Filato.
Har ila yau, wani abu da ya dauki hankali a yayin ziyarar shi ne batun kiran da ya yi ga kungiyar malaman jami’an kasar nan (ASUU) da ta janye yajin aikin da ta shafe watanni tana yi.
Ya nuna damuwa kan tasirin yajin aikin ga makomar ilimi da ci gaban Nijeriya, yana mai cewa yajin aikin nan ya kamata ya zo karshe haka nan.
Ya ce duk da ya fahimci bukatunsu, amma za a iya ci gaba da tattaunawa yayin da dalibai ke ajin karatunsu, wanda a cewarsa yajin aikin ba alkairi ne ga sashin ilimi da ci gaban tattalin arzikin kasa ba.
A wata sanarwar da kakakin shugaban kasan Malam Garbar Shehu ya fitar, shugaban kasan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya amshi bakoncin wasu gwamnonin jam’iyyar APC da wasu ‘yan majalisa da kuma ‘yan siyasa a lokacin da suka kai masa ziyarar barka da sallah a Daura.
Ya nuna damuwarsa da yajin aikin da ASUU ke cigaba da yi, inda ya nuna cewa iyaye da dama sun damu da zaman ‘ya’yansu a gida.
Shugaba Buhari ya nemi masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan da su sanya baki wajen ganin ASUU ta janye yajin aikin da take faman yi, inda ya ce duk wanda zai iya rokonta to ya taimaka ya yi hakan domin dalibai su koma makaranta.