Nadin Sarki Sanusi II: Ganduje Ya Yi Farar Dabara

A watan da ya gabata ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, don ya jagoranci wani babban kwamitin bayar da shawara kan samar wa da jihar hanyoyin zuba hannun jari, wato Kano Inbestment Adbisory Committee, wamda a ke yiwa lakabi da KanInbest. An dora wa kwamitin alhakin duba dabarun da za a iya yin amfani da su ne wajen ganin an samar wa da jihar yadda tattalin arzikinta zai sake karfafa ne.

A lokacin da gwamnan ya ke jawabi kan batun kafa kwamitin, ya bayyana cewa, an kafa shi ne domin a ci moriyar gogewa da kwarewar sarkin ya ke da ita a fannin sha’anin tattalin arziki, musamman a matsayinsa na tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya.

Tabbas wannan ba karamar farar dabara ba ce da Gwamna Ganduje ya yi, domin kuwa ba wai kawai mukamin gwamnan babban banki da Sarki Sanusi II ya rike ba, kwarewarsa a harkar ceto tattalin arziki daga durkushewa ita ce babbar damar da za a samu daga gare shi bisa la’akari da yadda tattalin arzikin jihohin kasar ke tangal-tangal, domin a tsawon shekarun da Mai Martaba Sarki ya shafe ya na aikin banki ya tabbatar wa da duniya cewa, ya na iya tserar da duk wani tattalin arziki da ya ke tangal-tangal kuma ya mike ya tsaya da kafarsa kyam!

A fili ta ke cewa, an ga yadda Sarki Sanusi II ya taimaki bankin UBA a lokacin da ya ke aiki tare da shi, musamman yadda ya jagoranci sashen kula da ‘Risk Management’ na bankin. Yawancin tsofaffin bankunan kasar a wancan lokacin sun kusa durkushewa, saboda zuwan sababbin bankuna da kuma juyawar yanayin tattalin arziki zuwa tsari na zamani, to amma da taimakon Malam Sanusi Lamido Sanusi (sunansa sarkin a wancan lokacin), sai bankin na UBA ya mike da kafafunsa.

Hakan bankin First Bank ya gani ya yi farar dabara irinta Ganduje ya dauke Sanusin kuma a karshe ya nada shi a matsayin shugabansa. A fili ta ke cewa, tun daga lokacin da Sanusi Lamidon ya jagoranci First Bank zuwa yanzu a na kallon bankin a matsayin daya daga cikin wadanda su ka fi kowanne tsaya wa da kafafunsu a fadin Afrika, ba ma Nijeriya kadai ba. Masana tattalin arzikin da harkar banki su na danganta hakan ne da kwazo da kwarewar Sarki Sanusin.

Babu shakka abinda tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa Yar’Adua, ya hasaso kenan ya nada shi a matsayin gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) duk kuwa da kasancewar an kai ma sa sunayen wadanda su ka fi Sanusin dadewa a aikin banki, irin su Alhaji Umar Abdulmutallab.

Wannan nadin da Yar’Adua ya yiwa Sanusi hakika ya kawo alheri mai tarin yawa, domin shi ne ya zo da sababbin manufofi, wadanda a yanzu ba ma kawai tattalin arzikin kasa ba, hatta sha’anin tsaro ya sake habaka, saboda tsarin sa Sanusi ya zo da shi a harkar bankunan kasar na tafi-da-gidanka, wato tsarin ‘cashless’. A yanzu duk inda za ka je ba sai ka dauki kudi a hannu ka na fargabar ’yan fashi ba, kawai ta wayarka za ka tura wa mutum.

Idan har gwamnatin jihar Kano ta bai wa kwamitin Sarki Sanusi II damar yin aiki yadda ya kamata, tabbas a kwai yiwuwar nan gaba kadan jihar za ta bunkasa fiye da yawancin jihohin kasar, musamman irin su Lagos da su ka yi nisa a dogaro da kai.

To, da ma da yawan mutane su na ganin cewa, nada Sanusin a matsayin sarki tamkar tauye Nijeriya ne, domin wasu gani su ke kamata ya yi a ce shi ne shugaban kasar, amma kasancewarsa ba zai ba wa ’yan kasar damar cin moriyarsa yadda ya kamata ba. To, akalla da irin wannan dama da masu rike da madafun ikon kasar za su rika bai wa mutane irin su Sanusi II, za a iya amfana da kwarewar tasu.

Don haka za a iya cewa, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne ya fi dacewa da ya aikata irin wannan farar dabara da Gwamna Ganduje na jihar Kano ya yi, domin bakidayan ’yan Nijeriya su cigaba da cin moriyar kwararru irin su Sanusi II, wadanda hatta kasashen duniya da hukumomi na duniya, kamar Bankin Duniya, su ka yarda da kwarewarsu da cancantarsu wajen rike mukamai.

Babban abin farin ciki a nan ga jihar Kano shi ne, yadda sarkin ya nuna ya amshi abin hannu bibbiyu, ya na mai cewa, “za mu sauke alhakin da a ka dora ma na mu na masu ji a jikinmu cewa tamkar kanmu ne. Mu na masu yaba wa gwamna bisa irin wannan kirkira mai cike da farar dabara da ya yi.”

Ashe kenan wadannan kalamai sun nuna cewa, a shirye sarkin ya ke da ya amshi duk wani aiki wanda zai iya taimaka wa al’ummar kasa, duk kuwa da cewa, akwai rawani a kansa! Ganduje ya yi farar dabara. Kalubale gare ka Shugaba Buhari wajen zakulo irin su Sarki!

Exit mobile version