Rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) da ke karkashin rundunar ta ‘Operation Fansan Yamma (OPFY)’ Sashe na 3 sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda a sassan Kakihun, Oke-Ode, Babanla da kewaye.
A wata sanarwa da mai magana da yawun NAF, Air Cdre Ehimen Ejodame, ya fitar, ya ce an gudanar da hare-hare-haren ne domin dakile barazanar ‘yan bindiga.
- Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka
- Jirgin Ƙasan Abuja–Kaduna Zai Dawo Aiki 1 Ga Oktoba – NRC
Ya tabbatar da cewa, Kwara ta sha fama da sabbin hare-hare daga ‘yan ta’adda a ‘yan kwanakin nan.
Sanarwar ta ce, wadannan hare-haren sun sake tabbatar da aniyar NAF na kare jami’an tsaro da fararen hula, da kuma ci gaba da matsin lamba kan masu tada kayar baya.
Ya kara da cewa, duk hare-haren an kammala su cikin nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp