Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce ta kashe ‘yan ta’adda kusan 600 cikin watanni takwas da suka gabata, waɗanda mafi yawansu a Jihar Borno ne.
Wannan na cikin ƙoƙarin da ake yi wajen murƙushe ƙungiyar Boko Haram da sauran masu tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabas.
- Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwamnan Zamfara
- Sin Ta Dauki Matakan Mayar Da Martani Kan Bankuna Biyu Na EU
Hare-haren sun kuma lalata sansanonin ‘yan ta’adda 166 da manyan motocin yaƙi sama da 200.
Duk da haka, matsalar tsaro har yanzu tana ci gaba da faruwa, ba kawai a Arewa maso Gabas ba, har ma da wasu yankuna na Arewa maso Yamma da Tsakiyar Nijeriya.
Masanin tsaro, Dokta Yahuza Getso, ya ce duk da nasarorin da sojoji suka samu, dole a ƙara tsananta matakan tsaro domin kawo ƙarshen matsalar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp