Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta tabbatar da cewa tawagar jiragen yaƙi na Operation FANSAR YAMMA ta lalata wata babbar mafakar ƴan ta’adda a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda aka hallaka da dama daga cikinsu. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar 15 ga Nuwamba 2025.
Ejodame ya bayyana cewa an kai hare-haren ne a ranar 14 ga Nuwamba 2025 bayan cikakken bincike da sa ido, ya tabbatar da cewa yan ta’addan suna amfani da sansanin Sauri a matsayin wurin ɓoye shanun da suka sace, ko ɓuya don kare kansu, da kuma wajen adana kayan aikinsu.
- Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano
- Gwamnatin Tarayya Na Yunƙurin Kawar Da Shanu Daga Titunan Abuja
Ya ce bayan samun ingantaccen bayanan sirri, jiragen yaƙi sun kai hare-hare a matakai da dama kan wuraren da aka tabbatar da ganin yan ta’addan, kuma an sami nasarar bugun wuraren kai tsaye, lamarin da ya tarwatsa waɗanda suka tsira suka yi yunƙurin gudu cikin dajin da ke kusa.
Ejodame ya ƙara da cewa an ci gaba da bin diddigin waɗanda suka tsere, inda dakarun suka sake kai musu farmaki har suka fatattake su gaba ɗaya. Ya ce wannan aiki ya yi nasarar hallaka da dama daga cikin ƴan ta’addan tare da rushe muhimman gine-gine da wuraren adana kayayyakin da suke amfani da su, wanda hakan ya raunana ƙarfinsu a yankin.
Ya ƙara da cewa Operation FANSAR YAMMA na ci gaba da tabbatar da cewa ƴan ta’adda ba su da mafaka a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya, domin dawo da zaman lafiya mai dorewa.














