Rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) karkashin shirin “Operation Fansan Yamma” ta kashe ‘yan ta’adda da dama a wani hari da ta kai ta sama a gidan wani kasurgumin jagoran ‘yan ta’adda da ke Palele a karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Olusola Akinboyewa, ya fitar ranar Litinin a Abuja.
- Xi Jinping: Alakar Sin Da Brazil Ta Kai Wani Muhimmin Mataki A Tarihi
- Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ya Nuna Yadda Sin Ta Yi Fice Wajen Ingiza Ci Gaba Da Farfadowa Da Gina Wadatar Bai Daya
Akinboyewa ya ce, an kai harin ne a ranar 16 ga watan Nuwamba, inda aka yi nasarar tarwatsa ma’ajiyar makamai da kuma gidan kasurgumin jagoran ‘yan bindiga, Malam Saleh – na dama-daman Dogo Gide.
Ya ce, ta’addancin Saleh ya addabi al’ummomin da ke yankin Shiroro, inda ya ke yawan kai hare-hare, da sace-sace, wanda hakan ya jefa tsoro da firgici cikin mazauna yankin.
A cewarsa, rundunar ta dade tana bin diddigin motsinsa (Malam Saleh), tare da tattara muhimman bayanan sirri don wargaza ayyukansa.