An gudanar da dandalin tattauna harkokin siyasa na bangarorin Sin da Amurka na bana a birnin Shenzhen, inda mahalarta daga bangarorin biyu suka zurfafa gudanar da managartan shawarwari, karkashin jigon “Hadin gwiwa da kalubale karkashin sabon yanayi: Tafarkin ci gaban alakar Sin da Amurka”.
Yayin zaman dandalin na jiya Lahadi, sassan biyu sun amince da cewa, samar da daidaito, da yanayi mai nagarta kuma mai dorewa na alakar Sin da Amurka, zai haifar da moriyar bai daya ga kasashe 2, kana hakan ne buri guda da daukacin sassan kasa da kasa ke fatan za a cimma. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp