Hukumar dake kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, ta kaddamar da sabbin jami’ai na musamman da za su rinka sanya ido domin dakile jabun magunguna a daukacin fadin kasar nan.
A jawabinta a wajen kaddamar da jami’an da aka gudanar a Abuja Dakarta Janar ta hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye ta sanar da cewa, akwai matukar bukatar a dauki matakan gaggawa, musamman domin a kare lafiyar ‘yan kasar wajen sayar masu da jabun magunguna, ba tare da saninsu ba.
- Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu
- Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa
Dokar hukumar ta Cap C 34 ce ta bai wa hukumar kafa jami’an na musmman, musamman domin a dakile sayar da jabun magunguna a kasar tare da kuma fadakar da alummar kasar, kan ilolin jabun magunguna.
Dakarta Janar ta hukumar ta bayyana cewa, wannan wani mataki ne, na gaggawa ga kara bayar da kulawa, ga fannin kiwon lafiya a kasar, musamman duba da cewa, rayuwar ‘yan kasa na shiga cikin hadari, idan ana sayar masu da jabun maguguna.
Duk a cikin namijin kokrin da NAFDAC ke ci gaba da yi na yakar jabun magunguna a fadin kasar, a tsakanin watannin Fabirairu zuwa na Maris din 2025 ta gudanar da wani gagarummin samame a wasu kasuwanni da ake sayar da magunguna a Onitsha da kuma a Ariaria.
A lokacin samamen ta samu nasarar kwace jabun magunguna da kuma lala magunguna da aka yo loda wa jabun magunguna sama da 100 da kudinsu ya kai na sama da Naira tirliyan daya.
Kazalika, an kama daruruwan masu sayar da magunguna tare da bankado jabun magunguna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp