Hukumar Kula da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa ta rufe wani kantin sayar da magani da ke Onitsha Crescent, Area 11 – Garki, Abuja, saboda sayar da magungunan da kwanan watansu ya kare da kuma marasa rijista.
An bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka wallafa ashafin D. Matakin dai ya biyo bayan wani rahoto da wani da abin ya shafa ya kai, lamarin da ya sa jami’an hukumar ta NAFDAC suka fara aiwatar da bincike. A yayin samamen, rundunar ta gano kayayyakin da kwanakin watansu suka kare wadanda darajarsu ta kai sama da Naira miliyan bakwai, da suka hada da na’urorin gwajin “H-Pylori”, wadanda ke haifar da babbar illa ga lafiyar al’umma.
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwaji A Kan Fasahar Sadarwa
- Sinawa Kimanin Miliyan 1.85 Za Su Rika Zuwa Yawon Bude Ido a Ketare Kullum Lokacin Hutun Bikin Bazara
An kama Manajan Daraktan kantin magani da wani babban jami’an domin amsa tambayoyi a wani bangare na binciken.
Sanarwar ta ce, “NAFDAC ta rufe wani kantin magani da ke Onitsha Crescent, Area 11 – Garki, Abuja, saboda sayar da magungunan da kwanakin amfani da su suka kare da kuma marasa rajista.
“Duk da kokarin da ma’aikatan kantin suka yi na kawo cikas ga aikin, rundunar ta yi nasarar kwace kayayyakin da lokutan amfani da suka kare tare da tsare wuraren.
“An kama Manajan Daraktan kantin da don ƙarin tambayoyi, yayin da za a sanya takunkumi mai tsauri a matsayin hana aikata ayyukan da ba su dace ba.
“NAFDAC ta bukaci jama’a da su sanya ido a lokacin da suke sayen kayayyakin da aka kayyade musu lokaci tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin NAFDAC mafi kusa.”