Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta lalata kayayyakin jabu, da marasa inganci, da wanda wa’adin aikinsa ya ƙare na kimanin Naira Miliyan ₦985.3m a jihar Kano.
Kayayyakin da aka lalata an karɓo su ne daga shiyyar Arewa maso Yamma, da suka haɗa da Kano da Katsina da Sokoto da Jigawa da Kaduna da kuma Zamfara, sun haɗa da magunguna marasa inganci, da kayan abinci marasa inganci, da kayan kwalliya, da sauran kayayyaki marasa inganci da hukumar NAFDAC ta haramta.
- A Guji Ajiye Abinci A Firji Fiye Da Kwana 3 – NAFDAC
- A Guji Ajiye Abinci A Firji Fiye Da Kwana 3 – NAFDAC
Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, wacce ta samu wakilcin shugaban shiyyar Arewa maso Yamma, Uwargida Josephine Dayilim, ta bayyana cewa kayayyakin da aka lalata sun haɗa da maganin kashe kwayoyin cuta, da maganin hawan jini, da maganin zazzabin cizon sauro, da maganin kashe kasala, magungunan ganye, da abubuwan sha, da kayan kwalliya, da dai sauransu.
Wasu daga cikin kayan da aka lalata dai wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu, da ƙungiyoyin Ƙwadago, da masu sayar da magunguna da kuma hukumar kwastam ta Najeriya ne suka miƙa su da kansa sakamakon ƙarewar wa’adin ingancinsu.
Hukumar ta jaddada ƙudirinta na kiyaye lafiyar jama’a da haɗa kai da masu ruwa da tsaki don tabbatar da sarrafa kayayyakin da aka kayyade.
A cewarta, NAFDAC na da burin kiyaye aminci, da ingancin kayan abinci da magungunan da ake samarwa ga jama’a ta hanyar ƙarfafa ayyukanta.
Shugaban hukumar ta NAFDAC na jihar, Kasim Ibrahim, ya yi ƙarin haske kan tasirin masu sayar da miyagun kwayoyi ke da shi a kasuwannin saye da sayarwa zuwa cibiyar hada-hadar (CWC) da ke kasuwar Dangwauro.
Lalata wannan kaya ya yi nasarar daƙile yaɗuwar jabun kayayyaki da marasa inganci a jihar, wanda hakan ya amfanar da ɗaukacin yankin da ma sauran yankunan makwabta.