Darakta Janar ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), Farfesa Moji Adeyeye, ta shawarci ‘yan Nijeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a firji na fiye da kwanaki uku saboda haɗarin kamuwa da cututtuka.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai na hukumar, Sayo Akintola ya fitar a ranar kiyaye abinci ta duniya ta 2024.
- Me Ya Sa Kamfanonin Waje Ke Neman Ci Gaba A Kasar Sin
- An Shawarci NAFDAC Ta Bullo Da Dabarun Fasaha Wajen Yaki Da Jabun Magunguna
Adeyeye, ta bayyana muhimmancin kiwon lafiyar jama’a da tattalin arziƙi da ke tattare da rashin tsaftataccen abinci, inda ta ce kusan mutane miliyan 600 ne a duk duniya suke fama da rashin lafiya a duk shekara sanadiyyar gurbataccen abinci, inda kusan 420,000 ke mutuwa.
An kiyasta nauyin tattalin arzikin duniya na waɗannan ayyukan abinci marasa aminci da dala biliyan 110 a kowace shekara, wanda galibi suna shafar ƙasashen da ba su ci gaba ba da masu tasowa ta hanyar asarar kayan aiki da kuma kashe kuɗin magani.
Ta jaddada cewa kiyaye abinci yana da muhimmanci ba kawai ga lafiyar jama’a ba har ma da ci gaban tattalin arziki da samar da wadataccen abinci.