Daraktar Kungiyar Fararen Hula na Kwamitin Yakin Neman Zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Najatu Muhammad, ta yi murabus daga mukaminta tare da ficewa daga APC.
Wannan na dauke cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar 19 ga watan Junairu, 2023 wanda ta aike zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, inda ta bayyana ficewarta a hukumance.
- Gobara Ta Jawo Wa Manoma Asarar Biliyoyin Naira A Ogun
- Za A Fuskanci Matsala Matukar Gwamnati Ta Hana Shigo Da Takin Zamani – Sarkin Noman Bassa
Naja’atu, ta ce kalubalen da Nijeriya ke fuskanta na bukatar ta ci gaba da fafutukar ganin an samar da kasa mai inganci ya sanya ta fice daga jam’iyyar.
“Wasikar ficewa daga jam’iyyar APC mai lamba 9.5 (i) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC, na rubuto muku ne domin na sanar da ku cewa na fice daga jam’iyyar APC,” kamar yadda wasikar ta bayyana.
“Ina sanar da ku game da yin murabus dina a matsayin Darakta Kamfen din shugaban kasa na APC. Babban abin alfahari ne yin aiki tare da ku don ba da gudummawa wajen gina al’ummarmu mai daraja.
“Duk da haka, da dama daga cikin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a fagen siyasa da dimokuradiyyar kasar nan, sun sa ba zan iya ci gaba da shiga harkokin siyasar jam’iyya APC ba.
“Kalubalen da Nijeriya ke fuskanta a yau na bukatar na ci gaba da fafutukar ganin an samar da ingantacciyar kasa da yanayi mai kyau.
Naja’atu ta fice daga jam’iyyar yayin da ke shirin shiga zaben shugaban kasa a wata mai kamawa.