Hajiya Aisha Abubakar, fitattaciyar manomiya ce kuma mai yin sharhi a kan al’amuran yau da kullum, wadda ta fito daga Jihar Kaduna. Kazalika, ita ce shugaba kuma wadda ta kirkiro da Gidauniyar Zulufat mai kare hakkin kananan yara da mata ta kasa. A tattaunawarta da wakilinmu; ABUBAKAR ABBA a Kaduna, ta yi bayani a kan nasarori da kalubalen yadda ta samu kanta a matsayin mace manomiya har ma da sauran wasu batutuwa da suka shafi mata.
Yaushe kika fara wannan sana’a ta noma?
Gaskiya shekarun da dama, kusan zan iya cewa kamar kimanin shekaru 25 kenan da na fara wannan sana’a ta noma. Sannan, na samu sha’awar fara yin noman ne, tun ina makarantar sakandire; lokacin muna aji daya akwai darasin aikin noma da ake koyar da mu, sai aka ba mu fili a makarantar don fara yin noman na gwaji.
A wannan lokaci, na fara da sayo Irin Alayyaho ne na shuka shi. Daga nan, sai na yi wa kanin mahaifina magana wanda ke zaune a karkara cewa, ina so na fara yin harkar noma; haka na rika turawa da kudi ana bai wa ‘yan kwadago suna yin min noman, bayan an girbi kuma sai a kawo min nan birni.
Amma wane lokaci kika fara yin noman gadan-gadan?
Ya zuwa yanzu dai, kusan shekara bakwai kenan da farawa gadan-gadan a matsayin sana’a, ina kuma matukar jin dadinta a yanzu cikin ikon Allah, domin kuwa a kullum kara fadada take yi.
Kamar wadanne irin amfanin gona kike nomawa?
Babban abin da na fi nomawa a gonar da ke Kauyen Kauya, cikin garin Afaka ta Jihar Kaduna ita ce Masara, wadda ina matukar jin dadin nomanta. Amma zai yi wuya ka ga manomi ya tsaya a kan abu daya. Kazalika, ina kuma yin noman Dawa, Shinkafa, Farin Wake, Waken Soya, a bana ma har da Agushi na shuka da kuma Dankalin Hausa.
Wadanne irin nasarori kike jin kin samu a wannan fanni?
Alhamdulillahi! Shi noma abu ne mai matukar amfani da kuma sirri a cikinsa, kusan na yi sana’o’i iri daban-daban tun bayan tasowata, amma duk a cikinsu gaskiya ban ga wadda ta kai wannan noma ba, domin shi noma kudi hannu ne; sabanin sauran sana’i’o da sai an hada da sayen kayanka bashi.
Har ila yau, noma na da albarka ga kuma lada, musamman yawan ‘yan kwadagon da za ka dauka su yi maka aiki a gonarka ka biya su, ka ga ko a nan ka rage zauna gari banza. Babbar nasara ita ce a ce yau kana taimaka wa mutane ta yadda za ka saukaka musu su tafiyar da rayuwarsu, wannan ita ce babbar nasara, wadda duk a cikin sana’ar ta fi yi min dadi.
Haka zalika, fitar da zakka ita ma wata nasara ce mai zaman kanta, mutane da dama za su ji dadi kwarai da gaske. Haka nan, shi ma Irin noman da za ka taimaka wa wani da shi; don shi ma ya samu ya shuka, shi ma babbar nasara ce. Kazalika, za ka bai wa mutane abinci su ma su ciyar da iyalansu, baya ga zakkar ita ma wannan nasara ce. Sannan, kai kanka manomin sana’ar na rufa maka asiri wajen warware matsalolinka na yau da kullum, musamman a yanzu da abincin yake matukar tsada, saboda haka a matsayinka na manomi, ba ma ta abincin da za ka ciyar da iyalanka kake yi ba, tuni ka wuce wannan wurin.
Wane kira za ki yi, musamman ga gwamnatin don kara karfafa harkokin aikin noma a fadin wannan kasa?
Ya kamata gwamnati ta kara kawata wannan fanni na noma, musamman ganin yadda matasanmu suke kammala babu aikin yi, su ma za su yi sha’arwar rungumar fanni, domin ganin nasu asirin ya rufu; mai makon jiran aikin gwamnati, domin a noma akwai albarka da kuma samun arziki mai dimbin yawa, wanda mutum ba zai iya ganewa ba, har sai ya samu kansa a ciki.
Ko za ki iya fada mana wasu daga cikin kalubalen da ki ke fuskanta a sana’ar?
Takin zamani na daya daga cikin wannan kalubale, don idan babu taki, gaskiya babu maganar noma; domin yadda farashinsa ke tashi a gaskiya mu manoma ba ma jin dadi; wasu manoman saboda tsadarsa, suke bayar da hayar gonakinsu a ba su ‘yan kudi kalilan; ka ga dai babu ranar fita daga talauci, wanda hakan ke kawo nakasu a aikin a Nijeriya.
Don haka, ya kamata a rika tallafa wa manoma ko da da wannan taki ne, gwamnati ta rika shigowa da shi tana sayar wa da manoma a kan farashi mai sauki. Sannan, ya kamata idan gwamnatin za ta rabar da takin; ta tabbata ya je hannun ainahin manoman, duk wanda ba manomi ba; gwamnati ta tabbatar da cewa, takin bai je hannunsa ba. Idan aka yi haka, za a samu sauki kuma abinci zai wadata a kasar.
Har ila ya, akwai matsalar yadda wasu masu kiwo ke sakin dabbobinsu; suna shiga cikin gonakin manoma suna cinye musu amfanin da suka shuka, duk da cewa; an yi shela a garin cewa kowa ya daure dabbobinsa, amma sai ka ga wasu suna sakaci wajen sakin dabbobin.
Maganar da ake yi yanzu, dole ne na sa a sake yin min feshe a gonar Dankalina, dalili kuwa bayan mun gama shuka; wasu sun saki Awakansu sun shiga gonar tamu sun yi mana barna. Ka ga wannan ba karamin kalubale ba ne. saboda haka, ya kamata makiyaya su rika jin tausayin manoma, tunda aikin namu na noma na da matukar wuya ga kuma kashe kudade masu yawa.
Kamar yadda na fada maka a baya, yau shekara bakwai kenan ina noma kamar hekta 23; amma yanzu sakamakon wannan rashin tsaro abin da nake nomawa kwata-kwata bai wuce hekta hudu ba, ka ga kuwa wannan ba karamin koma baya na samu ba.
A cikin hekta 23 kina samun buhunhuna kamar nawa?
Ina bai wa Masara hekta bakwai, inda nake samun kamar buhu 350 zuwa 400; sauran kuma Waken Soya nake shukawa da sauran amfanin, wanda wannan kuma sai abin da Allah ya ba ni; amma ba sa kai wa yawan na Masara. Amma a lokacin da babu rashin tsaro, ina noma kamar hekta 23. Yanzu saboda rashin tsaro, na dawo cikin gari kuma ka ga ba za ka samu girman gonar da kake so ka noma ba, yanzu kwata-kwata bai fi hekta hudu ba, don haka ka ga an ci baya kenan.
Yaya kike jin kanki a matsayin mace kuma manomiya?
Wallahi ina alfahari tare da jin dadi sosai da yadda Allah ya kaddara na zama daya daga cikin manoma mata. Domin a fannin noma, mata sun fi jajircewa da bin komai daki-daki fiye da maza; saboda haka da mata za su rungumi noma kamar yadda muka tsunduma a ciki, ba karamin abinci za a samar a wannan kasa ba, domin mu mata muna da juriya da hakuri wajen bin abu daki-daki, har mu ga mun kai ga cimma nasara.
Wane abu ne ya fi baki tsoro a wannan fanni?
Gaskiya, abin da ya fi ba ni tsoro ni da sauran daukacin manoma a fadin kasar nan shi ne, kalubalen rashin tsaro, wanda shi ne babban abin da ke firgita mu, manyan gonakin da ake da su wadanda ke samar da abinci mai yawan gaske a wannan kasa; amma sakamakon rashin tsaro sun kasa yin noma, wannan ko shakka babu ba karamin babban koma baya ne ga wannan fanni da kuma masu gonakin.
Karancin abinci da ake samu a Nijeiya, matukar ba a koma kan wadannan manyan gonakin ba, yunwa za ta iya kashe mutane. Wadannan su ne manyan abubuwan da na fi jin tsoro a wannan fanni na aikin noma.
A naki ganin, ina mafita ga hauhawar farashin kayan abinci a wannan kasa?
Mataki na farko dai shi ne, dukkanin abubuwan da suka kamata kama daga takin zamani, ingantaccen Iri da kuma yanayin aikin, ya kamata a saukaka su, musamman ma takin zamanin. Har ila ya, gwamnati ta tabbata ta magance rashin tsaro, domin rashin tsaron shi ne na farko, da zarar an magance shi, abinci zai wadata; farashin kayayyaki kuma ya sauka.
Kazalika, akwai kuma rashin tsaron da ake fuskanta a kasar; da ya sake jawo karancin abinci, wanda hakan yasa a kullum muke neman komawa matsayin hannu baka, hannu kwarya duk albarkar kasar nomar da Allah ya ba mu a kasar, bai kamata a ce hakan na faruwa ba.
Wace shawara za ki bai wa manoma, musamman ‘yan uwanki maza da mata?
Ina ba su hakuri tare da sake jan hankalinsu wajen kara jajircewa, domin kuwa noma na da wuyar gaske; in dai ba wurin da ake fama da rashin tsaro ba, zai yi matukar wahala ka ga manomi bai yi noma ba, matukar ruwan sama na sauka. Don haka, duk wurin da ya kasance akwai tsaro, manomi ya yi korari ya yi noma, amma duk wurin da babu tsaro ka da ka yarka ka kai kanka.
Sannan kuma, mu rika jin tsoron Allah a duk halin da muka tsinci kanmu, domin iya saukin da za mu yi wa al’umma bayan samun amfanin gona, zai sa mu ma Allah ya tausaya mana.