Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tana shirin tuntubar tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, domin ya dawo cikin jam’iyyar don haɗa kai wajen yaƙar jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027.
Muƙaddashin shugaban PDP, Ambasada Umar Damagun ne, ya bayyana hakan a wata hira da BBC, inda ya ce PDP a shirye ta ke ta karɓi duk wani ɗan jam’iyyar da ya bar ta.
- Shugaba Xi Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter
- Conceicao Ya Zama Sabon Kocin AC Milan Bayan Raba Gari Da Fonseca
Damagun, ya mayar da martani kan kalaman Kwankwaso na cewa PDP ta mutu, inda ya ce wannan ra’ayi ne kawai kuma ba gaskiya ba ne.
Ya ce PDP ta riga ta tsallake manyan ƙalubale tun daga 2015, lokacin da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka bar ta, amma hakan bai rusa ta ba.
Ya ƙara da cewa PDP ce kaɗai ke da ƙarfin cin zaɓe a Nijeriya idan aka cire jam’iyyar APC mai mulki.
Damagun ya ce, “Duk da kalaman da Kwankwaso ya yi, muna da yaƙinin cewa PDP ce ta haife sa kuma ta gina siyasarsa, har ya kai inda yake yau.
“Muna fatan zai dawo domin mu haɗa kai mu fuskanci wannan azzalumar gwamnati.”
Hakazalika, Damagun ya bayyana cewa jam’iyyar PDP tana da tarihin karɓar duk wani ɗan jam’iyyar da ya bar ta kuma ya dawo daga baya.
“A PDP, ba ma rufe ƙofa ga wanda ya tafi. Lokacin da ya dawo, muna karɓarsa kuma muna ba shi dama kamar sauran mambobi,” in ji shi.
Muƙaddashin shugaban ya kuma yi kira ga Kwankwaso da ya sake tunani game da batun haɗin kai da PDP, yana mai cewa jam’iyyar ce ta fi kowace damawa ga ‘yan Nijeriya.
Ya ce idan PDP ta mutu kamar yadda Kwankwaso ya faɗa, babu yadda za a yi ta ci gaba da samun gwamnoni da sanatoci a Nijeriya.
Damagun ya kammala da cewa nan ba da jimawa ba za su tuntuɓi Kwankwaso don tattaunawa da shi kan yadda za su yi aiki tare domin ceto Nijeriya daga matsalolin da ke damunta a yanzu.