Hukumar hana fataucin mutane ta kasa reshen jihar Kano, ta tseratar da wasu mata 12 dake da shekaru tsakanin 15 zuwa 50 daga kungiyar masu safarar mutane.
Kwamandan hukumar ta NAPTIP na shiyyar, Mista Abdullahi Babale, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin a Kano yayin da yake karbar wadanda aka ceton daga hukumar Hisbah ta jihar Kano, wadda ta gudanar da aikin ceton tare da hadin gwiwar hukumar.
- Firaministan Kasar Pakistan: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Hangen Nesa
- Tinubu Ya Yi Adalci Ga Dukkan Yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
A cewar Babale, an kama matan ne a ranar 31 ga watan Agusta a babban titin yammacin jihar Kano da ke Hotoro, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Ghana zuwa Saudiyya.
Ya bayyana cewa, matan sun fito ne daga jihohin Kano, Katsina, Borno, Jigawa, da Zamfara, inda aka yi musu alkawuran samun ingantattun ayyukan yi a kasar ta Saudiyya.
An kama daya daga cikin wadanda ake zargi da safarar matan mai suna Mohammed Saleh mai shekaru 45 da haihuwa.
Babale ya ce, ana ci gaba da kokarin damke wasu da ake zargi da hannu wajen safarar mutanen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp