Yaki da cin hanci shi ne babban kudurin da shugabannin kasar Sin suka sa a gaba,musamman bayan babban taro karo na 18 na wakilan jam’iyyar kwaminis mai mulki a kasar da aka gudanar a shekarar 2012, inda suka zage dantse wajen yaki da cin hanci a bisa doron halaccin tsarin siyasa.
Gwamanti mai ci a yanzu karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping duk da irin kalubalen da take fuskanta ta sami gagarumar nasara wajen fito da sabuwar dokar daukar hukunci mai tsanani ga duk wata harkar cin hanci da karbar rashawa a kasar.
A yunkurin kawo karshen cin hanci a kasar Sin, gwamnatin kasar ta yi nazari na tsanaki domin gano dalilai da kuma illar da cin hanci da rashawa suka yiwa kasar.
Irin matakin da kasar Sin ta dauka na kawo karshen cin hanci sun hada da kafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa tare da yin hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da aikata laifin cin hanci.
Hakika a wannan mataki kwalliya ta biya kudin sabulu domin gwamnati da jam’iyyar Kwaminisanci mai mulki sun hada karfi wuri guda wajen yakar cin hanci da kuma wanzar da hukunci kan doron shari’a ta yadda aka sami tsabtatacciyar gwamnati wadda babu bara gurbi a cikinta.
Irin matakan da gwamnatin ta Xi Jinping ta dauka da zummar cika burinta na kakkabe rashawa su ne kafa babban kwamitin binciko laifin cin rashawa na kasar.
Wannan kwamiti na binciko laifin cin rashawa ya zamanto kan gaba wajen gano ayyukan rashawa a kasar, inda ya binciko laifukan cin hanci da rashawa da kuma hukunta wadanda ke da hannu a ciki sama da mutane miliyan hudu a kowane matakin mukami na gwamnati.
Abin sha’awa a nan shi ne wannan kwamiti na binciko aikita laifin rashawa yana gabatar da wani shiri na kashin kansa mai suna “ba gudu babu ja baya wajen kauda rashawa” wato “zero tolerance” a Turance. Manufar wannan shiri ita ce nunawa ’yan kasa irin nasarar da kwamitin yake samu na yaki da karbar shawara tare da fallasa duk wani hamshakin gwamnati da aka samu da aikata laifin cin rashawa komai girman mukaminsa.
A rahoton kwamitin na shekarar 2018 zuwa ta 2020, kwamitin ya bayyana cewa ya yi nasarar kamo ’yan kasar da suka tsere zuwa kasashen ketare kimanin 3848, haka kuma an sami nasarar dawo da kusan biliyan goma na kudin kasar da aka yi awon gaba da su.
A hannu guda hukumar ta dauki matakan kau da cin hanci a kasar ta hanyoyi da dama, kadan daga ciki su ne, na daya, gwamantin kasar Sin ta bijiro da shirin ilmantar da ma’aikatan gwamnati kan rikon amana da kishin kasa ta yadda cin hanci da rashawa ba zai sami gurbi a cikin aikin gwamnati ba.
A dai wannan gabar gwamnatin ta tsara jadawalin ilimi a manhajar manyan makarantu na jami’o’i, makarantun sakandare da kuma makarantun firamare.
Duk wadannan matakai an dauke su ne da zimmar fahimtar da ‘yan kasa illar cin hanci da rashawa da kuma yadda suke rugurguza manufofin gwamnati na kyautata rayuwar ‘yan kasa.
Babu shakka irin wannan matakai da kasar Sin ta dauka sun taimaka kwarai da gaske wajen manufofin gwamnati na samar da rayuwa mai inganci ga ‘yan kasa.
Abin alfahari ga kasar ta Sin a yau shi ne yadda kasar ta yi bikin fidda miliyoyin ‘ya’yanta daga kangin talauci da fatara gami da kuma inganta rayuwar mazauna yankunan karkara, inda aka samar musu mazauni na zamani mai dauke da kayan alatu na more rayuwa kamar a manyan birane na kasar ta Sin.
A karshe wannan mataki na kauda cin hanci da rashawa da gwamnatin kasar Sin ta dauka karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping ya jawowa kasar ta Sin kima a idon sauran kasashen duniya, haka kuma irin ci gaban da kasar ta Sin ta samu a bangaren kimiyya da fasahar zamani ta zamanto gagara gasa a fagen kere-kere a duk fadin duniya. (Garba Shu’aibu Dakata)