• English
  • Business News
Saturday, September 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nasarorin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka A Shekaru Goman Baya

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Nasarorin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka A Shekaru Goman Baya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hulda dai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fara ne da dadewa tun a lokacin da kasar Sin tana hada hadar cinikayya da kasashen ketare a kan dadaddiyyar “hanyar siliki’’ da kuma lokacin gwagwarmayar neman ’yanci da Afirka ta yi fama da shi daga hannun ’yan mulkin mallaka daga farkon 1950 wanda kasar Sin ta yi rawar gani domin ganin kasashen Afirka sun samu ’yancin kai.

A sakamakon samun ’yancin da ci gaba da kulla huldar diplomasiyya ne kasashen na Sin da Afirka suka samu damar kulla zumunta wadda ta kai ga irin hadin gwiwar da ake da shi a yau, inda har sassan biyu suka kafa dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a shekarar 2000, wanda cikin shekaru sama da 20 da suka wuce, ya haifar da gaggaruman nasarori masu tarin yawa ga hadin gwiwar sassan biyu, tare da amfanawa al’ummunsu.

  • Wang Yi Ya Jagoranci Taron Manyan Wakilai Game Da Nazarin Matakan Aiwatar Da Manufofin Taron Ministocin FOCAC Na 8

A ci gaba da wannan dangantaka ne kasashen Afirka da dama suka shiga shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kirkiro a shekarar 2013, wadda aka fi sani da BRI wato “ziri daya da hanya daya’’.

Wannan shawara ta BRI ta samu karbuwa a yayin da kasashen Afirka sama da 50 suka rattaba hannu domin hadin gwiwar aiwatar da ita, shawarar tana kunshe da alfanu da tasiri da kuma tabbacin ci gaba na kasashe mambobi.

A karkasin shirin BRI wato “ziri daya da hanya daya”, a yanzu haka nasarorinsa sun bayyana kuma sun zama zahiri a idanun kowa.

Labarai Masu Nasaba

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

Makasudin wannan hadin gwiwar ta hanyar samar da tallafi ma kasashe masu tasowa dake da gibin kudaden gina ababen more rayuwa kamar hanyar jirgin kasa wato layin dogo da filayen jiragen sama da hanyoyin mota da tashoshin jiragen ruwa da dam-dam don samun wutar lantarki da ruwan sha da dai sauransu.

A sani na ne, kuma ni ganau ne ga nasarorin da irin hadin gwiwar Sin da Afirka suka cimma, har ma a ce a kasata Najeriya a shekaru goman da suka wuce.

A Najeriya dai hadin gwiwar ya haifar da gagaruman ci gaba ta fannoni da dama a kasar, kamar layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna da layin dogo na Lagos zuwa Ibadan da layin dogo mai zirga-zirga a cikin garin Abuja zuwa filin jirgin sama.

Haka zalika a karkashin wannan hadin gwiwar an samu kammala kayatar da filayen jiragen sama na zamani a manyan biranen Abuja da Lagos da Fatakwal da Kano. Akwai hanyoyin mota kamar hanyar Abuja zuwa Lafiya da kuma Kano zuwa Katsina wadanda yanzu haka aikinsu ya yi nisa.

Ba da jimawa da kaddamar da layin dogo na Abuja zuwa Kaduna ne na shiga wannan jirgin kasa zuwa Kaduna, lallai akwai kayatarwa domin wannan layin dogo shi ne na farko da ya hada Abuja da Kaduna.

Tafiyar dai ta bambamta da amfani da mota domin kuma akwai sauki. Hakazalika, akwai layin dogo mai zirga zirga a cikin Abuja wanda shi ma na dana shi zuwa filin jigin sama na Abuja.

Wannan layin dogon cikin gari akasari yana sufurin fasinjoji ne daga cikin garin Abuja zuwa tashar filin jirgin sama ta Abuja domin saukaka wa matafiya. Haka kuma ita ma sabuwar tashar jiragen sama da aka gina karkashin wannan hadin gwiwar na yi amfani da ita kuma tsarinta, da girmanta ya gamsu domin kuwa komai na zamani ne a cikinta kuma za ta ja da duk wata tashar jiragen sama a duniya.

Kasashe dai fiye da 35 a yanzu haka suke cin amfanin irin wannan hadin gwiwar kuma kwalliya na biyan kudin sabulu a duk inda aka fara gina wani abu, ko dasa wani abu a tsawon shekaru goma da suka wuce.

A kasar Habasha ma an samu babbar nasara a yayin da aka kammala layin dogo daga Addis Ababa zuwa tashar jirgin ruwa to Djibouti a farkon shekarar 2018. A kasar Kenya ma an yi nasarar kammala layin dogo daga babban birnin Nairobi zuwa tashar jirgin ruwa to Mombasa a shekarar 2017.

A Ghana ma an iyar gina Bui dam a shekarar 2013 wanda shi ne gagarumin aikin da hadin gwiwar Sin da kasar ta Ghana ta samu domin jin dadin jama’ar kasar.

Fahimta ta a kan wadannan nasarori a karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta nuna cewa kawance da dankon zumunci wadanda yana kamari tsakanin Sin da kasashen na Afirka kuma kasar Sin ta nuna cewa kasa ce da za’a iya dogaro da ita a kowane lokaci kuma cikin kowane irin halin da kawayenta na Afirka suka samu kansu a ciki, kuma ba da wasu sharuddan kaskantarwa ba ko tsoma baki a harkokin siyasa da na cikin gidan kowace kasa ba.

Fatarmu shi ne wannan dangantaka da aminci su dore domin kyautata zamantakewa tsakanin jama’ar mu baki daya. (Lawal Sale)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Rikicin NNPP: Kwankwaso Ya Ci Amanarmu – Shekarau

Next Post

Kulla Dangantaka Da Kasar Sin Domin Samun Sakamakon Moriyar Juna Cikin Sauri

Related

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya
Daga Birnin Sin

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

29 minutes ago
Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya
Daga Birnin Sin

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

1 hour ago
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin
Daga Birnin Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

2 hours ago
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin
Daga Birnin Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

3 hours ago
Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka
Daga Birnin Sin

Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

4 hours ago
Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154
Daga Birnin Sin

Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

5 hours ago
Next Post
Kulla Dangantaka Da Kasar Sin Domin Samun Sakamakon Moriyar Juna Cikin Sauri

Kulla Dangantaka Da Kasar Sin Domin Samun Sakamakon Moriyar Juna Cikin Sauri

LABARAI MASU NASABA

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

September 12, 2025
Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

September 12, 2025
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

September 12, 2025
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

September 12, 2025
Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

September 12, 2025
Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

September 12, 2025
Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

September 12, 2025
Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

September 12, 2025
Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan

Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan

September 12, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja

‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

September 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.