Hanta, wata tsokace mai matukar amfani a jikin Dan’adam, wadda ke taimakawa wajen lalata wasu kwayoyin jini gurvatattu ko wadanda suka lalace.
Ana samun wannan tsoka ne, a cikin cikin Dan’adam. Hanta dai, wata aba ce mai matukar amfani, wadda idan babu ita, katsokan za a iya cewa; babu mutum.
- Ribas: Ƙungiyar Ƙwadago Na Barazanar Shiga Yajin Aiki In Har Ba A Janye Dokar Ta-ɓaci Ba
- Amurka Ta Lahanta Taiwan Na Kasar Sin Ta Hanyar Sayarwa Yankin Da Makamai
Haka zalika, hanta mai lafiya kusan daidai take da mutum mai lafiya, haka nan kuma, hanta mara lafiya ma daidai take da mutum mara lafiya.
Kalolin Abinci Biyar Da Ke Lalata Hantar Dan’adam Sun Hada Da:
1-Abinci mai kitse
Dukkanin dangogin abinciccika masu kitse, na da matukar hadari ga lafiyar hantar Dan’adam. Abincin da ke da kitse, ya kan bai wa hanta wahala kwarai da gaske, kasantuwar cewa ita ce ke kula sarrafa dukkanin abin da ke shiga cikin Dan’adam. Don haka, yawan cin kitse na cutar da ita matuka gaya.
2- Siga
Kadan daga cikin ayyukan hanta shi ne, sarrafa siga zuwa sinadarin kitse, sannan kuma kamar yadda muka bayyana a sama, yawan hakan na da matukar lahali ga lafiyar hantar.
3- Gishiri
Binchiken masana ya nuna cewa, abinci mai gishiri kan yi lahali ga jiki, musamman ma dai kasantuwar hanta ita ce ke da alhakin sarrafa sinadarin. Yawan gishiri kan wahalar da hanta tare da sanya mata cuta.
4- Giya
Yawan shan giya, na taimakawa wajen lalata hantar Dan’adam, domin kuwa tana matukar wahalar da hantar wajen sarrafa ta.
5- Abincin Makulashe Na Gwangwani
Yawancin ire-iren wadannan abinciccika, na dauke da gishiri da siga mai tarin yawa, amfani da su din hakan kuma na matukar wahalar da hanta wajen sarrafawa.
Saboda haka, ya zama wajibi mutane su lura tare da kiyayewa, musamman wajen amfani da wadannan sinadarai. Duk abin da za a yi amfani da shi, a yi amfani da daidai-wadaida; kada a cika shi da yawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp