Ana noman lemon zaki a dukkanin fadin duniya, sannan kuma ya kasance daya daga cikin kayan lambun da za a iya shukawa a dan karamin waje ko a gidan gona, musamman idan yanayin wajen na da kyau.
Har ila yau, lemon zaki na dauke da sinadarin da ke karawa lafiyar jikin dan Adam lafiya, haka nan ana iya shuka shi a kowane yanayi na kakar noma, musamman daga watan Afirilu zuwa Mayu, har zuwa watan Disamba.
- An Gama Aikin Bitar Liyafar Bikin Bazara Karo Na 5 Ta Kasar Sin
- Mutane Sama Da Miliyan 43 Sun Kalli Bidiyon Dandanon Shirin Talibijin Na Murnar Bikin Bazara Na CMG Ta Kafar CNN
Yana da kyau ga wanda zai rungumi noman lemon zaki, ya tabbata ya samu ilimin shiga fannin, musamman idan har ya na so ya cimma nasara.
1- Samun Wajen Da Ya Da Ce Don Shuka Shi: Za a iya farawa da dan kadan, sannan daga bisani a fadada ta hanyar sayen gonar da za ta ci kimanin bishiyar lemon daga 40 zuwa 50.
Ya kamata a tabbatar da kasar noman ta na da kyau tare sinadaren da ya kamata a cikin ta, inda za a iya gane hakan ne, a lokacin da ake gyaran gonar. Haka zalika, ya kamata ka lura cewa; shin abin hawa zai iya shiga gonar cikin sauki, domin dakon lemon da ya nuna zuwa kasuwa, domin sayarwa.
2- Kasar Noman Da Ta Fi Dacewa A Shuka Lemon Zaki: An fi shuka shi a kasar noman da ruwa zai fi shigar ta sosai cikin sauki, sannan yin gwajin kasar noman na da kyau, don tabbatar da ganin tana da kyau wajen shuka lemon zakin ko kuma a’a?
3- Yanayin Da Ya Dace A Shuka Lemon Zaki: Lemon zaki ya fi saurin nuna a dausayi mai kyau, sannan ya na jure wa kowane irin yanayi.
4- Nau’ikan Lemon Zaki: Ya na da kyau a zabo nau’in da ya fi dacewa, don shukawa, musamman domin samun riba mai yawa. Haka nan, an fi so a shuka wanda zai fi saurin girma.
5- Yin Ban Ruwa: Kamar dai sauran kayan lambu, shi ma lemon zaki na bukatar a yi masa ban ruwa, domin idan ya na samun ruwa akai-akai, za a fi samun amfani mai yawa, haka kuma ya kan jurewa rashin samun ruwa.
6- Ya Na Da Kyau A San Yadda Lemo Ke Girma Daga Irinsa: Ya na da kyau a san yadda ya ke girma daga Irinsa, an kuma fi kuma yawan samun hakan ne a lokacin damuna, musamman ganin cewa, a lokacin ne aka fi samun wadataccen ruwan sama. Kazalika, ana kuma so a shuka Irin ya kai tsawon kimanin mita 1. 2, a kuma tabbatar da yana samun wadataccen haske rana tare da rika zuba masa taki a kalla sau daya a sati, domin ya yi saurin nuna.
7- Sanya Takin Zamani: Domin samun amfani mai yawa, ana iya zuba masa takin zamani, musamman don gudun ka da ya lalace bayan an shuka Irinsa.
8- Samar Wa Da Bishiyar Sarari: Ya na da kyau a sama wa bishiyoyinsa sarari, musamman don su dinga samun wadataccen hasken rana; ta yadda za su yi saurin girma, haka nan ana so a tabbatar da bishiyar tasa ta kai sararin fadin kafa 12 zuwa 25 a tsakanin juna.
9- Yadda Ya Kamata A Kula Da Bishiyar Lemon Zaki: Ya na bukatar a kula da shi yadda ya kamata kamar dai sauran kayan lambu, musamman domin ba shi kariya daga kamuwa da cututtuka ko kwari, sannan za a iya yin hakan ne ta hanyar samar da maganin feshin da ya fi da cewa.
10- Lokacin Da Ya Fi Dacewa AÂ Girbe Shi: A bisa hakikanin gaskiya, bishiyar lemon zaki na kai wa tsawon shekara daya kafin ya nuna, ana gane hakan ne bayan lemon ya fara faduwa kasa da kansa.
Kazalika, sauran da suka nuna a jikin bishiyar, za a iya cire su. Haka nan, an kiyasata cewa, ana iya cirar kimanin lemon zaki 50 a jikin kowace bishiya daya.