• English
  • Business News
Friday, August 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nazari Game Da Rayuwar Muhammadu Buhari

by Azu Ishiekwene, Sani Anwar and Muhammad
3 weeks ago
in Labarai
0
Nazari Game Da Rayuwar Muhammadu Buhari
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Na haxu da shi a lokuta da dama a bayan da ya zama shugaban qasa a 2015, amma haxuwar bai canza yadda na xauke shi ba tunda farko, a matsayin jajirtaccen mutum kuma tsayayye. In kuma aka shiga duba tarihinsa a nan ne za a fahimci cikakken yadda ya zama mutum mai sauqin kai a harkokinsa.

Mutum ne da bai san wasa ba, kamar yadda horon da ya samu a gidan soja ya yi tasiri a rayuwarsa kuma sune suka bayyana a harkokinsa na yau da kullum musamman siyasarsa.

  • Buhari 1942 – 2025: Rayuwarsa, Rasuwarsa, Jana’izarsa, Da Ci gaba Da Ta’aziyya
  • Tinubu Ya Isa Katsina Don Tarbar Gawar Buhari

Tasowarsa

An haife shi ne a ranar 17 ga watan Disambar 1942 a garin Daura da ke arewa maso yammacin Nijeriya yankin da a yanzu ke fama da ayyukan ‘yan ta’adda da masu aikata manyan laifuka. Buhari ya fara rayuwarsa na soja ne lokacin da ya shiga rundunar sojin Nijeriya a shekarar 1961. A wata tattaunawarsa da tsohon ministan sadarwa da tattalin arziqi, Sheikh Ali Pantami, ya bayyana cewa shiga sojar da ya yi, ya yi ne domin gujewa shirin yi masa aure da aka da wuri – wannan kuwa wata al’ada ce da ke gudana a yankin da ya fito har zuwa yanzu.

Wani vangare na labarin da ba a cika bayyanawa ba shi ne na cewa, ya rasa mahaifinsa tun yana xan qarami wanda hakan yasa ya rasa tallafi mai muhimmanci daga ‘yanuwa. Haka ya sa ya gujewa xaukar nauyin da bai shirya ba, wannan ne dalilinsa na shiga soja.

Labarai Masu Nasaba

Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 

Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo

Ya samu horon aikin soja a Nijeriya da Birtaniya da Indiya da kuma Amurka, ya yi yaqin basasan Nijeriya a qarqashin jagorancin Olusegun Obasanjo ‘Third Marine Commando Division’. Waxannan na daga cikin abubuwan da suka yi tasiri a ra’ayoyinsa na yadda ake tafiyar da al’umma ba tare da qa’ida ba da kuma yadda ya tsani rashawa.

A kan irin wannan ra’ayi nasa ne wasu jami’an soijoji da ba gamsu da yadda ake tafiyar da harkokin tattalin arziqin qasa ba suka sa ya jagorance su wajen hamvarar da gwamnatin fafrar hula ta Alhaji Shehu Shagari a shekarar 1983.

Waxannan sojojin ne kuma sune suka ga ya yi musu tsauri a yadda yake tafiyar da harkokin gwamanati, wataqila sun ga kamar ya fi su gaskiya, a kan haka suka yi masa juyin mulki na cikin gida kusan shekara biyu da mulkinsa. Daga nan aka kulle shi na tsawon shekara uku. Yana tsaren ne mahaifiyarsa ta rasu, buqatarsa na neman ya yi bankwana da gawarta bai samu ba wanda hakan na daga cikin abin da ya zafafa gaba a tsakaninsa da gwamnatin Babangida.

In banda wataqila Sardauna Ahmadu Bello ko Aminu Kano, babu wani a arewacin Nijeriya da yake da farin jinin al’umma kamar na Buhari. Halinsa na kasancewa mai gaskiya ya haifar masa da soyayya da mabiya a tsakanin talakawa. Talakawa suka zama jarinsa a siyasance, sun e suka kuma jawo shi siyasa abin da a da sai dai ya hange ta daga nesa.

Ximbin magoya bayansa a tsakanin talakawa ya sa manyan arewa suke tsoronsa musamman tun da sun rasa yarda da amincewa a tsakaninsu da talakawa. Da yawa sun yi amfani da wannan wajen xarewa karagar mulki, sun yi amfani da gaskiyar Burhari wajen kaiwa ga madafun iko.

Mutum ne mai nutsuwa, wanda ko kaxan babu wasa ko wargi a lamurukansa, Buhari ya kan yi wasu abubuwa da suka sava da tuniya ko ra’ayoyin abokanan siyasarsa. Kamewarsa ta daban ce, wadda ta qara masa kwarjini a tsakanin ‘yan siyasar Nijeriya. Rashin maganarsa a kan abubuwa da dama, wani baqon abu ne da ba a saba da shi ba, a yare irin na siyasa.

Tara Dukiya Da Fankama

Buhari ya kiyaye qima tare da mutuncinsa idon al’umma, ta hanyar rashin satar kuxin ‘yan qasa da fankama da kuma fariya. Ko shakka babu, ya yi ta faman gargaxin mutane da suka samu kansu a ofisoshi daban-daban, da su tsaya su rayuwa daidai samunsu.

Ana raxe-raxin rabuwarsa da matarsa ta farko da ta haifa masa ‘ya’ya biyar, Safinatu, ya biyo bayan wani almubazzaranci da matar Babangida, Maryam ta yi ne a kanta, yayin da yake tsare.

Har zuwa qarshe, babu soyayyar da aka rasa tsakanin Buhari da Babangida- lamarin da ya tava bayyana a fusace da Buhari ya amsa tambata game da rahoton kwamitin soja na da ya ba da shawarar tsige Babangida kafin juyin mulkin 1985.

Yunqurin da ya yi na inganta harkokin Mulki, wanda ya jaddada nisantar almubazzaranci da cin hanci da rashawa, ya zama babban qalubale a gwamnati farar hula, inda ya bayar da umarni; amma kuma ya kasa jajircewa tare da sanya ido a kai.

Yaqin da ya kasa yin nasara a kai

Duk da cewa, an kawar da mulkin soja; babban burin Buhari shi ne kawar da cin hanci da rashawa. Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya yi wa al’ummar qasar alqawarin samar da jirgin sama na qasa, wanda a qarshe al’amarin ya zama tamkar wasan kwaikwayo. Haka nan, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya yi barazana qwarai da gaske tare da batun zartar da hukuncin kisa ga jami’an da aka samu dumu-dumu wajen aikata cin hanci da rashawa. Duk da zaton da aka yi wa Buhari na xaukar tsattsauran mataki, amma bai yi komai a kai ba.

Mutumin da manyan masu faxa a ji da kafafen yaxa labarai ke kallonsa a matsayin xan kama-karya, Buhari ya yi qaqarin nuna cewa; ya sauya zuwa cikakken wanda ya yi amanna ga tsarin demokuraxiyya.

Buhari ne fa yana zaune yana kallon wasu tsirarun jam’iyyu suna raba muqamai a tsakanin sojoji, majalisar ministocin tarayya da zavavvun hukumomin tarayya da ke qarqashin kulawar majalisar dokoki ta qasa, duk da cewa ja,’iyyarsa ce Mulki.

Waxanda aka naxa a majalisar ministocin, sun yi amfani da irin wannan rashin gaskiya, musamman ‘yan siyasar da suke da matuqar gogewa na tsawon shekaru a tsarin. Sai dai kuma, abin yabo ne a gare shi cewa; rashin tsoma baki a kan al’amuran jam’iyya da kuma tsarin dokoki, ya sake qarfafa demokuraxiyya.

Rikicin 12 ga Yuni

Ogan Buhari a soja, Olusegun Obasanjo, shi ne ya girbe rigingimun siyasar da suka faru a 12 ga watan Yuni da hannunsa, wanda ka iya kawo rashin daidaito a tsarin siyasar Nijeriya. Amma kuma Buhari a nasa vangaren, ya xauki matakan da suka dace, domin warware abubuwan da suka zama ruxani a taswirar siyasar qasar.

Har ila yau, haka ya ci gaba da warware matsaloli iri daban-daban, kamar daidaita tsoffin waxanda suka yi yaqin basasar Nijeriya a vangaren Biafra, waxanda aka yi watsi da su; biyan bashin ma’aikatan kamfanin jiragen Nigeriya da gwamnatin Obasanjo ta bari tare kuma da cika alqawuran da gwamnatocin baya ta yi wa qungiyar qwallon qafa ta qasa, bayan shafe shekaru da dama ana yaudarar su.

Babbar sa’ar da ya samu

Buhari ya lashe zaven shugabancin qasa a 2015, sai abin ya zama kamar wani busa, inda faxuwar man fetir ya haifar da koma bayan vangaren tattalin arziqin da ya gada. Qasar ta yi matuqar fuskantar manyan-manyan qalubale sosai, waxanda suka yi tasiri wajen haqo mai, inda matasa a yankin Neja Delta mai arziqin man fetur, yankin da wanda Buharin ya gada ya fito; suka riqa faman yin zagon qasa a matsayin ramuwar gayya ga 2015.

Haka nan, a farkon wa’adinsa na biyu, duniya ta sami vullar cutar Korona, wacce ta da ta shafi tattalin arziqin da tuni ya kusa ya kusa durqushewa. Dokar hana fitar da aka sanya dalilin vullar wannan cuta ya zafafa hauhawar farashin kayayyaki kuma ya shafi qoqarin Buhari na bunqasa noman abinci a cikin gida.

Hangen nesa

Hangen nesan Buhari ya mayar da hankali ne sosai kan yaqi da cin hanci da rashawa da tsaro, wani lokacin kuma a kan manyan -manyan batutuwan da suka shafi mulki. Bayan Shekara 30 da da barinsa mulki ya sake dawowa, al’amuransa sun daidaita kamar yadda ya yi a baya idan aka kwatanta da sauran waxanda suka yi mulki a baya.

Amma hakan ya kawo cikas bisa ga yadda gwamnatinsa ta xauki matakin magance qalubalen zamantakewa da tattalin arziki daban-daban. Batutuwa kamar hanyoyin kiwo da wuraren kiwo sun zama wuraren tashe-tashen hankula wajen daidaita yanayin siyasar da riga ya yi rauni, baya ga fahimtar son zuciya a naxin muqamai na siyasa.

Yanayin nuna halin ko-in-kula da ya dabaibaye fadar shugaban qasa Buhari, ya qara fitowa fili wajen nuna lallai Buhari ya tabbata da kammala wa’adinsa na biyu. Domin Buhari bai damu da gwagwarmayar maye gurbi a cikin jam’iyyarsa da kuma salon siyasar gwamnan babban bankinsa ba, wanda ya fito da tsarin canza fasalin kuxin qasar nan na son zuciya, Buhari ya sanya hannu ne tare da ko ya amince ko da rashin amincewarsa ne. Sakamakon kuma ya bayyana a zavukan qasa da suka biyo baya.

Shugaban qasa ba shi da satifiket na makaranta

’Yan adawa sun qirqiri hotunan qarya da yaxa jita-jita cewa Buhari ya mutu, wani mutum wai shi “Jibril daga Sudan” ne ya riqa yaxa hoton a Aso Rock. Gogaggun ‘yan siyasa suka ci gaba da yaxa jita-jitar shugaban qasa bai da mata kuma ya kamata ya auri xaya daga cikin ministocinsa a matsayin sabuwar mata har ma da buga katin gayyata.

Wannan ya faru ne saboda kawaicin da Buhari ya yi na wuce gona da iri. Ko kuma wani lokacin, ta hanyar jin haushinsa.

‘Baba Go-Slow’

Misali, lokacin da na ziyarce shi tare da na hannun damansa kuma shugaban LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, watanni kaxan bayan zaven 2015, mun yi ta barkwanci da Buhari. A ranar Lahadi ce jaridar The Guardian na cikin tarin jaridu da ke kan teburi a ranar. Ya daxe a yana duba wani shafi a jaridar LEADERSHIP.

“Ya kalli Nda wanda shi ne mai kamfanin LEADERSHIP, Ya ce Nda waye kunkuru a wannan zanen”? Inda ya amsa cewa “Ranka ya daxe kai ne.”

An yi wa zanen zanen laqabi da ‘Baba Go-Slow’, wani sharhi da ya yi nun da cewa ya shafe watanni yana naxa majalisar ministocinsa.

“Kana nufin wannan ni ne?” Buhari ya fashe da dariya. Ganin halin da qasar ke ciki a lokacin, Buhari naku ne.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: DauraGwamnatin jihar KatsinaKatsinaRasuwar BuhariRayuwar Buhari
ShareTweetSendShare
Previous Post

Wata Motar Tankar Mai Ta Kama Da Wuta Tare Da Kone Wasu Motoci A Ibadan, Jihar Oyo

Next Post

Akwai Bukatar Daina Cin Zarafin Malaman Makaranta

Related

Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 
Labarai

Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 

12 minutes ago
Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo
Labarai

Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo

43 minutes ago
Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Manyan Labarai

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

11 hours ago
Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 
Labarai

Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

12 hours ago
Neja
Labarai

Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago

13 hours ago
Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana
Labarai

Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

14 hours ago
Next Post
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Akwai Bukatar Daina Cin Zarafin Malaman Makaranta

LABARAI MASU NASABA

Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 

Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 

August 8, 2025
Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo

Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo

August 8, 2025
Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 

Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 

August 7, 2025
Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

August 7, 2025
Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

August 7, 2025
Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

August 7, 2025
Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

August 7, 2025
Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

August 7, 2025
Neja

Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago

August 7, 2025
Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

August 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.