1. Ana Bukatar Tabbatar Da Samun Yanayin Da Ya Fi Dacewa:
Noman Kanumfari, na bukatar ma’aunin yanayin da ya kai kasa da 59 °F (15 °C), amma an fi son ma’aunin yanayin da ya kai daga70 zuwa ma’aunin yanayin da ya kai 85 °F (21 to 29 °C).
Har ila yau, Bishiyarsa na bukatar zafin da ya kai daga kashi 60 zuwa kashi 70.
2. Shuka Irin Kanumfari:
Manomin da zai shuka Irin noman Kanumfari, ana bukatar ya sa hakuri, idan har kana bai wa Bishiyarsa kulawar da ta dace, za ta iya shafe tsawon shekara 100 ko sama da haka.
Ana bukatar wanda zai shuka shi, ya tabbatar ya shuka Irin noman a kasar noma mai inganci, sannan kuma yana daukar dogon lokaci kafin ya kammala girma.
3. Ba Shi Kulawar Da Ta Kamata:
Ana iya shuka Irin noman Kanumfari a gida, kuma zai iya yin girma; amma ya fi bukatar yanayin da yake da zafi, haka nan ko da an shuka shi a yanayin da ya dace, yana kai wa tsawon shekara bakwai kafin ya kammala girma, kazalika, ana bukatar wanda ya shuka Irin noman, ya tabbatar da amfanin na samun hasken rana a kullum, har Ila yau, iska mai karfi na yi wa Bishiyarsa illa, musamman a lokacin da take tasowa.
4. Ba a son wanda zai shuka Irin nomansa, ya shuka wanda ya bushe, domin matukar aka bar Irin ya bushe, ba zai taba girma ba.
5. Ba a son wanda zai noma shi, ya bar Irin a cikin rana, ana bukatar ya samar masa wajen da ya fi da cewa tare da yi masa ban-ruwa akai-akwai, haka nan, ana so a bar Irin ya girma har zuwa wata shida, bayan an shuka shi kafin a canza masa wajen da za a sake shuka shi, haka yawan yi masa ban-ruwa na iya jawo mutuwar Irin da aka shuka shi.
6. Ana son Irin nomansa da aka shuka, akalla ya kai daga wata 18 zuwa wata 24, kafin a canza masa wani wajen, haka Irin nomansa na girma ne a hankali, amma ana bukatar Irin ya kasance ya yi karfi sosai, don ya samu sukunin dorewarsa, musamman idan an shuka Irin a fili.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp