Alamu sun nuna cewa, a ‘yan kwanukan baya an samu wani sauki, a zirga-zirgar Jirgin kasa a kasar nan, musamman saboda samar da karin wasu manyan hanyoyi.
Kazalika, bisa kokarin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da yin a habaka fitar da kaya zuwa ketare da kuma kara samarwa da kasar kudaden musaya, hakan ya sanya Gwamnatin ta mayar da hankali wajen ingnata wasu daga titin Dogo na kasar.
- Janar Murtala Mohammed: Ba Rabo Da Gwani Ba…
- Xi Ya Jaddada Hada Karfi Da Karfe Wajen Gina Kyakkyawar Kasar Sin
Fannin sufuri, na daga cikin fannonin da ke da mahimmanci wajen kara bunkasa tattalin arziki da samar da ci gaba.
An yin amfani da Jiragen kasa wajen yin safarar, kamar ma’adanan kasa, kayan abinci, kayan da aka sarrafa, da tura kayan aikin gona da sauransu.
A saboda haka, akwai bukatar a samar da sabbin kayan aiki domin a inganta titunanan na Dogo, musamman domin a kara samarwa da kasar kudaden shiga.
Jaridar BusinessDay tayi nazari kan manyan ayyuka biyar na Layukan Dogo da suka samar wani sauki, a zirga-zirgar Jirgin kasa a kasar nan.
1 Layin Dogo Daga Legas Zuwa Ibadan
Ingantaccen aikin layin Dogo mai tsawon kilomita 157 da ya taso daga jihar Legas zuwa garin Ibadan.
An faro aikin ne a watan Maris na 2017 aka kuma kaddamar da shi, a ranar 10 na watan Yununin 2021.
Aikin ya kasance mai tagwayen hanya biyu da ake da shi, Afrika ta Yamma.
An kammala aikin layin na Dogon ne, cikin shekaru hudu, wanda kuma aka kara fadada shi zuwa kimanin kilomita 7 domin ya hade da layin Dogo na tashar Jirgen Ruwa da ke Apapa.
Wannan layin Dogon, na bayar da gudunmawa wajen kara bunkasa hada-hadar kasuwancin yankunan da ke makwabtaka da wannan layi Dogon.
2. Layin Dogo Daga Abuja Zuwa Kaduna
Layin Dogo da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, aiki ne, da aka yi da kaya aiki na zamani wanda kuma ya kai tsawon jimlar kilomita 186.5. Kzakila, an tsara aikin ne, yadda Jirgin kasa zai yi gudun da ya kai kilomita 150.
3. Jirgin kasa Mai Amfani Da Lantarki A Cikin Birinin Legas:
A wannan layin Jirgin kasan na na hada Legas da jihar Ogun wanda gwamnan jihar ta Ogun Dapo Abiodun, ya kara ware Naira tiriliyan daya a cikin kasarin kudi na 2025.
Kashi na farko na aikin, na da Tashoshi biyar kuma ya na yin zirga-zirgar da a ka ta tsawon kilomita 13, da aka bude a ranar 4 na watan Satumbar 2023.
Kazalika, babbar Layin Dogon, zai kasance mai tsawon kilomita 27, wanda ake sa ran a kullum zai yi jigilar fasinjoji 500,000.
4 Jirgin kasa Mai Amfani Da Lantarki A Cikin Birinin Tarayyar Abuja:
Kusan aikinsa ya kasance ne a cikin birnin Abuja, wanda kuma shi ne, Jirgin kasa na farko, mai gudu a kasar, kuma na biyu a Afirka ta Yamma.
Kashin aikin na farko, an kaddamar aikin ne a rana 12 na watan Yulin 2018 wanda zai hada tashar filin tashi da saukar Jigin sama ta Nnamdi Azikiwe, inda kuma zai tsaya a tashar Jirgin kasa da ta Idu da ta tashi daga Abuja zuwa Kaduna.
Aikin Jirgin kasa Na Fatakwal Zuwa Maiduguri:
Wannan aikin ya lashe dala biliyan 3.2 ana kuma sa ran zai hada Kudu da Arewa Maso Gabas tare da layukan rassan Owerri da Damaturu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp