ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ana Zargin Wani Ɗansanda Da Kisan Wata Mata Kan Cin Hancin Naira 2,000 — Bincike

by Rabi'u Ali Indabawa
1 year ago
Dansanda

Wani korarren dansanda, Aremu Musiliu, wanda ake zargi da kashe wata mata mai shayarwa mai suna Comfort Udoh, ya bace bayan da ya karbi beli a asirce daga babbar kotun Jihar Legas, kamar yadda binciken jaridar PUNCH Metro ya gano.

Musiliu, tare da wasu ‘yansanda biyar, an yi zargin sun harbi babur mai kafa uku a unguwar Isheri a shekarar 2015, wanda mijin Comfort, Godwin Udoh ke tukawa.

  • Dansandan Da Ya Ki Karbar Cin Hancin Miliyan 150 Ya Samu Shatara Ta Arziki
  • Dokar Ta-ɓaci A Ribas: GwamnoninPDP Sun Ƙalubalanci Hukuncin Tinubu A Kotun Ƙoli

Rahotanni sun ce babur din na dauke Comfort ne da ‘ya’yanta hudu, ciki har da wani jariri dan watanni hudu a lokacin da suke dawowa gida daga wani shiri na coci.

ADVERTISEMENT

Duk da sun bayyana cewa su ba matafiya ba ne sun nufi gida ne kawai bayan kammala ibada, Musiliu ya dage kan sai an ba shi cin hancin Naira 2,000 kafin ya bar su su wuce.

A lokacin da daya daga cikin ‘yan sandan da ke shingen binciken ya umurci dangin su tafi, Musiliu ya ce ya harba makaminsa kan babur din.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Harbin dai ya samu Comfort ne a kai, inda nan take ta mutu, yayin da wasu harsasai suka samu mijinta a mukamuki da kafadarsa dama.

Yayin da ‘ya’yansu ke kururuwar firgici, rahotanni sun ce jami’an sun gudu daga wurin.

An kori Musiliu daga aikin ‘yansanda ne a ranar 17 ga watan Satumba, 2015, daga bisani kuma aka bayar da belinsa a shekarar 2017 ba tare da sanin dangin da ya kashewa ‘yan uwa ba.

Bayanan kotun sun nuna cewa mai shari’a O.A. Taiwo na Kotun 26, Babban Kotun Ikeja, ya bayar da belin Musiliu a kan Naira miliyan 1 tare da mutane biyu.

A hukuncin kotun, Mai shari’a Taiwo ya bayyana cewa, “Sashe na 115(1) na dokar shari’a ta shekarar 2011 ya bai wa kotu damar bayar da belin wanda ake tuhuma da laifin kisa.

“Don haka kotu na da hurumin bayar da belin wanda ake tuhuma da laifin kisa ko kuma a’a, hakkin mai nema ne ya nuna ta hanyar bayar da wasu bukatu na musamman wadanda za su bai wa kotu damar yin amfani da damar da ta ga ya dace ga mai bukata.”

Tun lokacin da aka bayar da belin Musiliu, jaridar PUNCH Metro ta gano cewa har yanzu ba a san inda Musiliu yake ba duk da zaman kotun da aka yi da kuma yunkurin kama wadanda za su tsaya masa.

Da yake zantawa da jaridar PUNCH, Godwin Udoh ya bayyana takaicinsa da irin wannan rashin imani.

“Na yi mamaki da ban gan shi (dan sandan) a kotu ba kafin daga baya na gano cewa an bayar da belinsa, babu wanda ya yi tsammanin za a bayar da belinsa.

“Duk lokacin da suka nemi gidan yarin da su gabatar da shi a gaban kotu, sai su ba da uzuri kamar rashin man da za su yi jigilarsa. A haka na fara binciken abin da ke faruwa,” in ji Udoh.

Udoh ya bayyana cewa binciken da ya yi ne ya sa ya gane cewa lallai an saki Musiliu.

“Kotun da ke tafiyar da shari’ar a yanzu tana babbar kotun TBS, amma ba su taba kawo shi wurin domin gurfanar da shi ba, lokacin da aka taba gurfanar da shi a gaban kotun majistare da ke Ebute Metta a shekarar 2015 da lamarin ya faru,” in ji shi.

“Alkalin mai shari’a, Hon. Justice Akintoye, har ma ya rubuta wa dukkan gidajen yarin Jihar Legas wasiku, amma sun ki gabatar da wannan mutum a kotu, har ma sun bayar da sammacin kama mutum biyun da za su tsaya masa.

Udoh ya koka da cewa, “Kotun gaba daya ba ta yarda an bayar da belinsa ba, sai da ni kaina na je na gano shi, a lokacin ne na tabbatar da cewa kotun Honarabul Taiwo da ke Ikeja ta bayar da belinsa, yanzu mutumin ya bace, ba mu sake jin komai a kansa ba.”

Har yanzu dai ana ci gaba da shari’ar, inda aka shirya zaman kotu na gaba a ranar 9 ga watan Afrilu, sai dai Udoh bai da tabbas ko za a yi adalci.

“Babu wanda ya tsaya masa a kotu a matsayin lauyansa, sai dai mai gabatar da kara daga ma’aikatar shari’a ta Jihar Legas ya ce in yi kokarin ganin su a Alausa domin su samu hanyar gurfanar da shi a gaban kotu,” in ji shi.

Udoh, yayin da yake tunani a kan rayuwarsa bayan wani mummunan lamari da ya faru a shekarar 2015, ya bayyana cewa an bar shi da ‘ya’yansa suna kokawa su kadai, duk da alkawuran da shugabannin ‘yansanda suka dauka na tallafa musu.

“Ciwon da nake ji daga wannan rauni har yanzu ba na iya jurewa,” in ji shi.

“Har yanzu akwai wani karfe a cikin mukamukina da ya kamata a cire, likitan ya ce suna bukatar fitar da shi a maye gurbinsa da kashi don in iya tauna da kyau. Amma yayin da nake magana da ku, karfen yana ci gaba da cutar da ni.

Udoh ya kuma tunatar da yadda ‘yansanda suka kasa taimakawa wajen binne matarsa marigayiya a shekarar 2016.

“Na gana da kwamishinan ‘yansandan Jihar Legas, amma ya ce min ‘yansanda ba sa binne kowa kuma in yi da kaina,” in ji shi.

Ya koka da cewa duk da tabbacin da ‘yansandan suka yi sun yi watsi da shi da iyalansa.

“Sun yi alkawari za su kula da ni, da biyan duk kudin da nake kashewa na jinya, da kuma tabbatar da cewa an yi mini tiyatar da ta dace, amma sun bar ni ina shan wahala.

“Kudin aikin cire wannan karfe daga mukamukina ya kai miliyoyin Naira, kuma ba ni da wannan kudin,” in ji shi.

Udoh ya ci gaba da bayyana cewa, rundunar ‘yansandan ta kuma yi alkawarin tallafa wa ‘ya’yansa na kudi, kula da lafiya, da bayar da tallafin karatu.

“Sun ce za su saka ni a cikin lissafin albashi don in sami akalla tallafin kudi a kowace shekara. Babu wani abu da ya faru,” in ji shi.

Hatta takardar shedar karatu da aka bai wa ‘ya’yansa daga baya an dawo da su.

“Sun ce kuskure ne kuma za su gyara su mayar da shi ga sufeto-janar domin ya amince min, har yau ban samu ba.”

Ta’asar da ‘yansanda ke yi wa fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba ya zama ruwan dare duk da kokarin da ake na shawo kan jami’an da ke da ra’ayin aikata laifuka.

Rundunar ‘yansandan ta kori Sufeto Usman Dikko daga mukaminsa bisa rasuwar Baale na Lotu, Marigayi Cif Fatai Jubril, a shekarar 2023.

An kori wani jami’in da ya yi wa wata yarinya fyade da bindiga a cikin ofishin ‘yansanda a Legas.

Dansanda
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

MASU ALAKA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221
Labarai

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
Next Post
Kogin Rima Zai Bunƙasa Noma Da Haɓaka Tattalin Arziƙi – Abubakar Malam

Kogin Rima Zai Bunƙasa Noma Da Haɓaka Tattalin Arziƙi - Abubakar Malam

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.