A lokacin noman rani, musamman ga masu son shuka mangoro, wajibi ne masu yin nomansa su tabbata suna yi masa ban-ruwa, tun daga lokacin da ya fara fitar da fure, har zuwa lokacin da zai nuna.
Wasu daga cikin manomansa, sun fi son su fara yi masa ban- ruwa bayan bishiyarsa ta kai kashi 50 da fara fitar da fure, inda akalla furen zai fara budewa.
Bugu da kari, wasu manoman nasa kuma, suna fara yi masa ban-ruwa ne, bayan sun ga furen ya fara fitowa, inda suke yin hakan domin furen ya yi saurin girma.
Har ila yau, yawan irin ban-ruwan da za a yi masa; ya danganta da irin girman da bishiyar ta mangwaron ke da shi.
Kazalika, yin ban-ruwan ya danganata da irin kasar noman da aka shuka mangwaron da kuma irin karfin jijiyarsa.
Don haka, ana so a dan dakatar da yi masa ban-ruwa har zuwa wasu ‘yan makwanni, wato kafin a yi masa girbi.
Sinadaran da ya kamata a yi amfani da su:
Sai dai, mangwaro na jurewa yin girma a cikin kowane irin yanayi, sannan kuma bai cika samun wasu kalubale wajen samun harbin kwayoyin cututtuka ba.
Sinadaran da ake yi wa mangwaro feshi da su, ya danganta ne da irin cututtukan da suka harbe shi.
Wasu daga cikin sinadaran feshin sun hada da kamar irin su ‘Potassium’.
Zuba takin zamani:
Takin zamanin da ake zuba wa mangwaro, ya danganta da irin matakin da ya kai na yin girma.
Wadannan su ne tsarin da aka bayar da shawa kan sinadaran da ke sanya mangwaro ya girma.
A shekara ta farko, ana bukatar a zuba masa sinadarin ‘Calcium Ammonium Nitrate’ da ya kai kimanin kilo 100.
A shekara ta uku, ‘Calcium Ammonium Nitrate’ daga kilo 150 zuwa 300.
A sauran shekarun da suka biyo baya kuma, ana so a zuba masa sinadarin ‘Calcium Ammonium Nitrate’ da ya kai kimanin kilo 200 zuwa 400.
Haka zalika, a matakin farko bayan shekaru hudu, ana so a zuba masa sinadarin ‘Compost’, inda za a hada da takin gargajiya domin ya kara hababa, inda akalla ake so a zuba masa takin gargajiya da ya kai kimanin kilo 10.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp