Kwanan baya, na kai ziyara kauyen Bapo, kauye ne na al’ummar kabilar Jino da da ke yankin Xishuangbanna na lardin Yunnan dake kudu masu yammacin Sin, inda na ga an rataya hoton tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong a kofar gidajen mazauna kauyen, kuma Miko wadda ke rayuwa a kauyen ta fada min cewa, dalilin hakan shi ne don bayyana godiya da amincewarsu ga gwamnatin Sin.
Ta ce, a watan Oktoba na shekarar 1952 bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta tura tawagogin aiki zuwa sassan dake fama da matukar talauci da ke karkarar lardin Yunnan. Ma’aikatan tawagogin sun yi rayuwa da aiki tare da mazauna wuri, sun yi ayyuka da suka hada da gina madatsar ruwa da gidaje, da aikin debo ruwa da daka shimkafa, kana sun taimakawa al’ummar wuri a mabambantan harkoki, wanda hakan ya sa al’ummar Jino suka fita daga zamantakewar al’umma irin ta zamanin da da can.
- Waƙa Sana’a Ce Sai Da Ilimi Da Jari -Wizzamany
- Jihar Filato Ta Yi Hadaka Da Kasar Bulgeriya A Fannin Noma
A halin yanzu, iri wadannan tawagogi na ci gaba da aikinsu a tsaunuka dake Xishuangbanna, kuma ma’aikatan sun gaji ruhi daga tsoffinsu, suna kokarin fitar da hanyoyi mafiya dacewa na farfado da kauyuka da raya sana’o’in wurin. Har ma mazauna wuri su kan ce, yadda ba za a bar gishiri a rayuwa ba, hakan nan ma ba za a bar tawagogin ba.
Miko ta ce, a da zaman rayuwar al’ummar Jino ya godara ne kan aikin farauta, kuma al’ummar Jino suna shuka ganyen shayi don biyan bukatunsu ne kawai. Amma daga baya gwamnatin wurin ta yi amfani da fifikon da al’ummar Jino ke da shi don kyautata zaman rayuwarsu, inda ta gabatar da tsarin “Kauye daya haja daya”, don raya tattalin arzikin wurin.
Misali kauyen Bapo da na ziyarta, na dogaro da al’adun ‘yan kabilar Jino masu ban sha’awa, da ma ganyen shayi na Pu’er mai inganci, abin da ya sa ya zama kauyen da ya shahara a bangaren yawon shakatawa bisa al’adunsa a Yunnan.
A shekarar 2019, al’ummar Jino sun fita daga kangin talauci gaba daya. Miko ta gaya min cewa, a yanzu tsoffin gidaje dake cikin tsauni sun kasance wani sashi na bayyana al’adun Jino, bayan mutanen da a baya ke rayuwa cikinsu sun kaura zuwa gidaje na zamani.
Daga zamantakewar al’umma irin ta zamanin da da can, zuwa samun bunkasuwa irin ta zamani, daga gidaje marasa inganci zuwa gidaje masu inganci, daga sufurin kayayyaki ta amfani da doki zuwa motoci, zaman rayuwar al’ummar Jino na samun kyautatuwa matuka. Na zauna a gida mai rataye da hoton marigayi Mao Zedong, ina dandana shayin Pu’er, ina ganin cewa, al’ummar Jino sun tabbatar da bunkasuwa cikin sauri karkashin manufar kawar da talauci da gwamnatin kasar Sin ta dauka. A halin yanzu kuma, al’ummar Jino na kokarin kama hanyar zamanintar da kan su. (Mai zane da rubuta: MINA)