Zomo dabba ce da ke da saurin sabo da jama’a, kana kuma namansa na da matukar dadi tare da karawa jikin Dan’adam lafiya, musamman duba da cewa, yana dauke da ‘sinadarin protein’.
Saboda haka, yana da kyau ga mai kiwan sa; ya rika ba shi kulawa yadda ya kamata tare kuma da sanin lokacin da yake sauya dab’arsa.
- Jan Kafar Tinubu Na Cire Harajin Shigo Da Abinci Na Ci Gaba Da Ta’azzara rayuwa
- Cimma Burin Rage Salwantar Abinci A Kasar Sin Zai Samar Da Mafita Ga Duniya
Akwai cututtuka takwas da ka iya harbin Zomo da kuma hanyoyin magance su.
1- Harbi A Kunne:
Akwai wata cuta da a turance ake kira da ‘mites’ da ke harbin sa a kunne, wadda take sanya masa jin kaikayi.
Ana magance wannan cuta ne, ta hanyar yawan duba kunnen nasa a kullum; don ba shi kariyar da ta kamata.
Kazalka, ana yakar cutar ne; ta hanyar rika shafa masa mai a wurin da cutar ta harbe shi.
2- Cutar Da Ke Fito Masa A Kan Hanci:
Akasari wannan cuta da a turance ake kiran ta da ‘Snuffles Rabbit’, ta na fito masa ne a kan Hanci; wanda hakan ke sanya wa yake fitar da majina ko kuma Idonsa ya rika fitar da ruwa.
Ana dakile wannan cuta, ta hanyar ciyar da Zomon abinci mai gina jiki tare kuma da tabbatar da ana tsaftace wajen kwanansa.
3- Tsananin Zafin Da Ke Rage Masa Kuzari:
Wannan cuta wacce a turance ake kira da ‘Heat Stroke’, na sanya masa rashin walwala; ana kuma so mai kiwon sa ya tabbatar yana lura da wannan cuta.
Ana dakile cutar ne, ta hanyar ajiye Zomon a cikin inuwa tare da kare shi da ajiye shi a cikin hasken rana.
4- Cutar Da Ke Harbin Sa A Kafa:
Idan ka lura da wannan cuta, wacce a turance ake kira da ‘Sore Hocks’, za ka ga Zomon yana jin zafi a kafarsa, sannan kuma a cikin sauki, ana iya warkar da ita.
Ana kare shi daga kamuwa da wannan cuta, ta hanyar sanya masa raga a wajen barcinsa ko kuma sanya masa tabarma; don ya rika dora kafarsa.
5- Cutar Da Ke Harbin ‘Ya’yan Hanjinsa:
Wannan cuta da ake kira ‘Bloat’, idan ta harbi Zomo tana yin sanadiyyar mutuwar sa; ana kuma yawan samun ta tare da Zomaye.
Kazalika, cutar tana sanya masa kumburin jiki.
Ana dakile ta ne kuma ta hanyar yawan duba yanayin da Zomon yake gudanar da rayuwarsa.
6- Cutar ‘Coccidiosis’:
Wata cuta sananniya ce wadda ke harbin Zomo, tana farauwa ne idan Zomon ya fara yin gudawa, inda cutar ke shafar hantar Zomon da ya kamu, inda kuma cutar ke hana su cin abinci da kasa shan ruwa.
7- Cutar Da Ke Sanya Kan Zomo Ko Wuyansa Yawan Kadawa:
Wannan cuta da ake kira ‘Head Tilt’, sananniya ce da ke harbin Zomo.
8- Fitsarinsa Na Komawa Ja:
Akwai cutar da ke harbin sa, wacce ke sany fitsarinsa ya koma ja ko ruwan dorawa.
Don haka, idan mai kiwon ya ga haka; kada ya ji tsoro mai yiwuwa yana cin abinci ne da yawa kamar Karas.
Sai dai, idan yana samun sauyin abinci ko kuma sun ci gaba da yin irin wannan kalar fitsari, bayan an sauya masa abincin ana bukatar mai kiwon ya dauki wani nau’i na fitsarin nasa; don yin gwaji.